Badakalar N18bn: EFCC Ta Sake Shigar da Sabuwar Kara Kan Godwin Emefiele

Badakalar N18bn: EFCC Ta Sake Shigar da Sabuwar Kara Kan Godwin Emefiele

  • Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta sake shigar da ƙara kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
  • Hukumar yaƙi da cin hancin na ƙarar Emefiele kan zargin buga takardun kuɗi na N684m bisa zunzurutun kuɗi har N18.96bn
  • An shigar da sabuwar ƙarar ne kan tsohon gwamnan na bankin CBN a gaban mai shari'a Hamza Muazu na babbar kotun tarayya da ke Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta sake shigar da sabuwar ƙara kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

EFCC ta shigar da sabuwar ƙarar ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

Yadda hukumar EFCC ta samu nasarar kwato N120bn cikin watanni 6

EFCC ta sake shigar da kara kan Emefiele
EFCC ta shigar da sabuwar kara kan Godwin Emefiele Hoto: @cenbank, @officialEFCC
Asali: Twitter

Wane zargi ake yi wa Emefiele?

Jaridar Daily Trust ta ce a cikin sabuwar ƙarar, an zargi tsohon gwamnan na CBN da sanya hannu wajen buga kuɗin da suka kai Naira miliyan 684,590,000 kan kudi Naira biliyan 18.96.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta ce Emefiele ya karya doka ne da nufin cutar da jama'a a yayin da yake aiwatar da tsarin sauya fasalin kuɗi na gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ta gabata, cewar rahoton jaridar The Punch.

A cikin ƙarar, EFCC ta kuma yi zargin cewa Emefiele, a lokacin da yake kan mulki, ya amince da cire Naira biliyan 124.8 ba bisa ƙa'ida ba daga asusun tara kuɗaɗen shiga na tarayya.

Yaushe EFCC ta shigar da Emefiele ƙara?

A cewar babban mai shigar da ƙara na EFCC, Rotimi Oyedepo SAN, a cikin ƙarar mai lamba: CR/264/2024, mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Afirilu, 2024, Emefiele zai gurfana a gaban kotu bisa sababbin tuhume-tuhume huɗu a gaban mai shari’a Hamza Muazu.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Za a gurfanar da shi ne kan zargin rashin biyayya ga doka domin wahalar da ƴan Najeriya, cin zarafin kuɗi, buga kuɗi ba bisa ƙa'ida ba, da sauransu.

Idan ba a samu wani sauyi ba, za a gurfanar da Emefiele ne a gaban babbar kotun tarayyar da ke Abuja, a ranar 30 ga watan Afirilun 2024.

An umurci EFCC ta tsare Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Legas mai zama a Ikeja ta umurci hukuma EFCC ta tsare Godwin Emefiele a hannunta.

Alƙalin kotun shi ne ya bada umurmin a tsare Emefiele a kurkukun EFCC bayan an gurfanar da shi kan zargin hannu a almundahanar $5.5bn da N2.8bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel