Fursunoni 118 Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali a Jihar Neja, an Samu Bayanai

Fursunoni 118 Sun Tsere Daga Gidan Gyaran Hali a Jihar Neja, an Samu Bayanai

  • Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja
  • Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Laraba yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ya lalata katangar gidan yarin
  • Ya zuwa yanzu dai ba a tantance adadin fursunonin da suka gudu ba, amma an tura jami'an tsaro domin kamo wadanda suka tsere

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Suleja, jihar Neja - Akalla fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren Laraba.

Kara karanta wannan

An cafko fursusoni 10 cikin wadanda suka tsere a Neja, ana ci gaba da neman sauran

Fursunoni sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar Neja.
Sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, fursunoni sun tsere a gidan yarin Neja.
Asali: UGC

Fursunoni sun tsere daga gidan yari

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa fursunoni da adadinsu ya kai 118 sun yi amfani da damar ruwan sama wajen tserewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwan saman da ya mamaye ko'ina a cikin garuruwan Neja da ma makwaftakan garuruwan birnin tarayya Abuja ya lalata wasu sassan katangar gidan yarin.

Wani mazaunin garin Abdullahi Nura ya shaida wa manema labarai cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke bakin aiki inda suka tsere ta bangarori daban-daban.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin fursunonin sun yi amfani da duwatsu wajen tarwatsa mutanen da suka kawo agaji agaji domin hana su tserewa.

Gidan yari: Jami'an tsaro sun dauki mataki

A halin yanzu an baza tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa cikin garin Suleja domin kamo fursunonin da suka tsere, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da manyan mutane daga Abuja ya ci karo da cikas, ya fantsama daji

Wani mazaunin garin Suleja, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce:

“Gaskiya ne lamarin ya faru, mun taimaka wajen cafke biyu daga cikin fursunonin, kuma mun mika su ga hukumar gidan yarin."

An kuma tattaro cewa jami’an tsaro na ta harbe-harbe a saman iska domin tsoratar da fursunonin da suka tsere su fito daga maboyarsu.

Channels TV ta ruwaito cewa an dan samu nutsuwa yanzu yayin mutane suka ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullum yayin da ake ci gaba da neman fursunonin.

Gwamnati za ta cefanar da DisCos

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala shiri na sayar da kamfanonin kasuwa da ke rarraba wutar lantarki (DisCos).

Gwamnati ta ce bankuna da kamfanin AMCON da ke tafiyar da lamuran kamfanonin rarraba wutar sun gaza biyan basussuka, haka kuma wutar lantarki ta ki zama a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel