Lambar Ministan Tinubu Ta Fito Kan Zargin Yin Cushen N30bn a Kasafin Wata Hukuma

Lambar Ministan Tinubu Ta Fito Kan Zargin Yin Cushen N30bn a Kasafin Wata Hukuma

  • Ana zargin Heineken Lokpobiri, ƙaramin ministan man fetur na Shugaba Bola Tinubu da yunƙurin yin cushen N30bn a kasafin kuɗin hukumar NCDMB
  • Simbi Wabote, wanda shine tsohon shugaban hukumar NCDMB, ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar
  • A martanin da ministan ya mayar, ya ce tsohon shugaban NCDMB na fama da jin zafin tsige shi daga muƙaminsa, wanda ya shafe shekaru bakwai a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Yenagoa, jihar Bayelsa - An zargi ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri, da ƙoƙarin yin cushe a kasafin kuɗin hukumar NCDMB na shekarar 2024.

Simbi Wabote, wanda shi ne tsohon shugaban hukumar NCDMB, ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya aikowa Legit.ng.

Kara karanta wannan

Filato: Soja da ke shagalin ƙara shekara ya bindige wani bawan Allah har lahira

An zargi ministan Tinubu da yin cushe a kasafin kudi
An zargi Heineken Lokpobiri da yin cushe a kasafin kudin hukumar NCDMB Hoto: @DOlusegun, @senlokpobiri
Asali: Twitter

Simbi ya ce ministan ya matsa masa lamba kan ya ƙara kasafin kuɗin ofishinsa da Naira biliyan 30 a watan Disamban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi ministan Tinubu da cushen N30bn

Simbi Wabote ya yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, inda ya musanta zargin da ministan ya yi a baya na cewa ya yi almubazzaranci da dala miliyan 500 na zuba jari da lamuni a hukumar.

A martanin da ya mayar, ministan ya zargi tsohon shugaban NCDMB da cewa har yanzu yana jin zafin rasa muƙaminsa, duk da ya shafe shekara bakwai a hukumar.

A cewar jaridar This Day, mai ba Lokpobiri shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Nneamaka Okafor, ya mayar wa Simbi martani a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jihohi 10 da farashin litar man fetur ya fi arha a Najeriya

Nneamaka ya bayyana martanin da Simbi ya mayar a matsayin wani lamari na “idan ka yaƙi cin hanci da rashawa, cin hanci da rashawa zai yaƙe ka."

Me ministan Tinubu ya ce kan zargin?

Yayin da yake amsa tambayoyi a wurin wani taro a Legas, Lokpobiri ya yi zargin cewa Simbi ya riƙa saka hannun jari mara kyau a lokacin da yake jagorantar al'amuran NCDMB.

Ministan ya ce sama da Dala miliyan 500 na lamuni da aka bayar a kamfanoni masu zaman kansu sun salwanta a ƙarƙashin kulawar Simbi.

A cewar ministan, NCDMB ta zuba sama da dala miliyan 190 a wasu ayyuka masu zaman kansu a ɓangaren man fetur da iskar gas da suka haɗa da kamfanin takin zamani na Brass da kuma matatar mai ta Atlantic, duk a jihar Bayelsa.

Ya ce an salwantar da ayyukan ne saboda babu wani gini a wuraren biyu.

An gargaɗi Shugaba Tinubu

Kara karanta wannan

Badakalar kudi: Hukumar EFCC ta tsare mai neman takarar gwamnan jihar Ondo

A wani labarin kuma, gamayyar jam'iyyun siyasa ta UPPP reshen jihar Kogi ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan dambarwar Yahaya Bello.

Ƙungiyar ta buƙaci Tinubu ya ja kunnen hukumar EFCC game da yadda ta ke gudanar da bincikenta kan tsohon gwamnan na jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel