Zulum Ya Ba Sojoji Shawara Kan Hanyar da Za a Kawo Karshen Rashin Tsaro a Borno

Zulum Ya Ba Sojoji Shawara Kan Hanyar da Za a Kawo Karshen Rashin Tsaro a Borno

  • Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi magana kan rashin tsaron da jiharsa ra daɗe tana fama da shi na tsawon shekaru
  • Gwamnan ya buƙaci rundunar sojojin Najeriya da ta kafa sansanin sojoji a dajin Sambisa, gaɓar tafkin Chadi da tsaunin Mandara
  • A cewar gwamnan yin hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda a jihar wacce ta yi iyaka da ƙasashe uku

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya buƙaci sojojin Najeriya da su samar da sansanin sojoji a dajin Sambisa domin magance matsalar ayyukan ta'addanci na ƴan ta'adda.

Gwamna Babagana Zulum ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin ziyarar da 'yan kwamtin harkokin sojoji a majalisar wakilai suka kai birnin Maiduguri, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Zulum ya bukaci a kafa sansanin sojoji a Sambisa
Gwamna Zulum ya bukaci sojoji su kafa sansani a dajin Sambisa Hoto: Babagana Umara Zulum, HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Wace shawara Gwamna Zulum ya bada?

Gwamnan na jihar Borno ya nuna buƙatar da ke akwai ta sojoji su samar da sansani a gaɓar tafkin Chadi da tsaunin Mandara, inda ƴan ta'adda ke ci gaba da samun mafaka, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dangane da batun kawo ƙarshen rashin tsaro gaba ɗaya, akwai buƙatar gwamnati ta kafa sansanin sojoji a dajin Sambisa, tsaunin Mandara da gaɓar tafkin Chadi."

- Babagana Umara Zulum

Ya buƙaci majalisar wakilai da ta tabbatar ana ware kaso mai tsoka na siyo makamai domin magance matsalar rashin tsaro.

Zulum ya kuma koka kan yadda iyakokin jihar Borno suke, da buƙatar a tsare jihar wacce ta yi iyaka da ƙasashe uku domin magance matsalar ƙwararowar ƙananan makamai waɗanda ke ƙara rura wutar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Jaridar The Guardian ta ce ya kuma ƙara jaddada aniyarsa ta tallafa wa sojoji a hanyoyin da suke bi wajen magance matsalar rashin tsaro, inda ya ƙara da cewa kawo yanzu, tubabbun ƴan Boko Haram 190,000 ne suka miƙa wuya ga hukuma.

Kara karanta wannan

'Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da gurfanar da ƴan ta'addan da ta kama a gaban kotu'

Gwamna Zulum ya bada tallafin karatu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta sanar da fara biyan ɗaliban jinya da unguwar-zoma tallafin karatu ga kowanne dalibi har N30,000 duk wata a fadin jihar.

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar wanda ya bayyana hakan ya bada tabbacin cewa ɗalibai 997 da suka fito daga jihar ne zasu amfana da tallafin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel