Manyan Labarai A Yau
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ba jam'iyyarsa ta PDP shawara kan hanyar dawowa kan madafun ikon kasar nan a zaben 2027 da ke tafe.
An samu aukuwar wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Sokoto. Jirgin ruwan ya kife ne dauke da fasinjoji. Masu iyo sun samu nasarar ceto wasu daga cikin mutanen.
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta cafke wani dan kasuwa dauke da hodar iblis mai yawa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
Akalla kasashe shida a nahiyar Afirka ne suka katse haɗin guiwar tsaro ko suka kori sojojin Faransa daga iyakokinsu, mafi yawan kasashen na karkashin soji.
An samu tashin wata mummunar gobara a wata babbar kasuwa da ke birnin Gusau a jihar Zamfara. Gobarar ta lakume shaguna masu yawa a kasuwar ta babura.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyara a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina. Gwamnan ya duba marasa lafiya tare da ba su tallafin kudi.
Gwamnatin tarayya za ta gyara gidajen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Ƙashim Shettima. An ware biliyoyin Naira domin gudanar da ayyukan a kasafin 2025.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babaganaa Umara Zulum, ya samar da motocin da za su yi jigilar bakin da ke zaune a jihar wadanda za su yi tafiya domin bikin Kirsimeti.
Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya koma APC. Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Imo ya koma APC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari