Sarki Mai Martaba Ya Shiga Siyasa da Kafar Hagu, Gwamna Ya Sauke Shi daga Sarauta

Sarki Mai Martaba Ya Shiga Siyasa da Kafar Hagu, Gwamna Ya Sauke Shi daga Sarauta

  • Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya dakatar da Sarkin Iselu na Masarautar Iselu, Oba Akintunde Akinyemi, nan take bisa zargin shiga harkokin siyasa
  • An sanar da dakatarwar ne a ranar 20 ga Oktoba, 2026, ta hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin sarauta, Ganiyu Hamzat
  • Gwamnatin jihar Ogun ta ce matakin ya biyo bayan korafe-korafe da dama kan halayen sarkin, musamman zargin shiga harkokin siyasa a fili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya dakatar da Sarkin Iselu na Ƙaramar Hukumar Yewa ta Arewa, Oba Akintunde Akinyemi, nan take bisa zargin shiga harkokin siyasa na jam’iyyu.

Gwamna Abiodun ya sanar da dakatarwar ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 20 ga Oktoba, 2026, wadda Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Ganiyu Hamzat, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Zargin shirin hallaka Atiku ya je Amurka, za a kai korafi ga Trump

Gwamnan jihar Ogun.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun a fadar gwamnatinsa Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar Zartarwa ta Jihar Ogun ce ta amince da dakatarwar bisa sashe na 52(1) na Dokar Sarakuna da Hakimai ta Jihar Ogun ta 2021.

Gwamnan Ogun ya dakatar da sarki

Wasiƙar ta bayyana cewa majalisar ta ɗauki matakin ne bayan samun “korafe-korafe da dama kan halayen sarkin, musamman zargin shiga harkokin siyasa na jam’iyyu a fili, waɗanda wasu daga cikinsu shi da kansa ya yaɗa su.”

Gwamnatin ta bayyana cewa shiga siyasar jam’iyyu ya saɓa wa dokokin al’ada kuma doka ta haramta shi ga kowane basarake a jihar Ogun.

Ta yi gargaɗin cewa irin wannan hali na iya rage martabar sarautar gargajiya tare da kawo barazana ga zaman lafiya tsakanin al’ummar da ke da goyon bayan jam’iyyun siyasa daban-daban.

Ta ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, da shugabanci nagari a Jihar Ogun, musamman a Masarautar Iselu, yayin da ake gudanar da bincike a hukumance kan zarge-zargen.

Kara karanta wannan

Gani ga wane: Gwaman ya raba Sarki da rawani, fadarsa kan tsunduma kansa a siyasa

Umarnin da aka ba sarkin

A matsayin wani ɓangare na sharuɗɗan dakatarwar, an umarci Oba Akinyemi da ya bar fadarsa, sannan kada ya sake shiga cikinta a duk tsawon lokacin da dakatarwar za ta yi aiki.

Haka kuma, an umurci basaraken da kada ya ci gaba da gabatar da kansa ko da'awar cewa ana amincewa da shi a matsayin Sarkin Iselu.

Ogun.
Taswirar jihar Ogun da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wasiƙar ta kuma umarci sarkin da ya kasance a shirye domin halartar duk wani taro ko zaman bincike da gwamnatin jihar za ta kira domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa.

Gwamna Abiodun ya fara rabon tallafi

Kun ji cewa gwamnatin jihar Ogun, tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da Bankin Duniya, ta fara rabon N6bn ga kungiyoyin mata 3,855.

Gwamna Dapo Abiodun ya ce kudin ba tallafi ne na kyauta ba, sai dai wani tsarin samar da jari da zai taimaka wajen kafawa da fadada sana’o’i.

An kaddamar da rabon kudin ne a Ijebu-Ode, inda aka bayyana cewa shirin na da nufin bunkasa kasuwancin mata, karfafa tattalin arzikin gidaje da kara shigar mata cikin harkokin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262