An Cire Shugaban Hukuma bayan Ya Jawo 'Abin Kunya' ga Tinubu da Shugabannin Tsaro

An Cire Shugaban Hukuma bayan Ya Jawo 'Abin Kunya' ga Tinubu da Shugabannin Tsaro

  • An sauya shugaban Hukumar Fansho ta Sojoji, Air Vice Marshal Mikail Abdulraheem, bayan zanga-zangar tsofaffin sojojin Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa takaddamar da ta barke tsakanin ɓangarorin biyu ta ba shugabannin sojoji da fadar shugaban ƙasa kunya
  • Tsofaffin jami’an soji sun zargi hukumar da yin kuskuren lissafin kuɗaɗen fanshonsu da sauran haƙƙoƙinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kasa da mako guda bayan wani saɓani mai zafi tsakanin shugaban Hukumar Fansho ta Sojoji da tsofaffin jami’an rundunonin sojin Najeriya, am fara daukar mataki.

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin soji sun sauya shugaban hukumar fanshon sojoji saboda abin da ya faru, wanda ya haifar da zanga-zangar tsofaffin jami'ai.

Babban hafsan tsaro.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: DHQ Nigeria
Source: Twitter

Majiyoyin da suka san da batun sun shaida wa Daily Trust cewa an ɗauki takaddamar da ta faru tsakanin hukumar fanshonda tsofaffin jami’an sojin a matsayin abin kunya.

Kara karanta wannan

Zargin shirin hallaka Atiku ya je Amurka, za a kai korafi ga Trump

Sun ce lamarin ya zama kamar abin kunya ga manyan shugabannin sojoji da kuma shugaban ƙasa, wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojin ƙasar.

Abin da ya faru tun farko

Legit Hausa ta ruwaito cewa a ranar Talatar makon da ya gabata, saɓanin da ke tsakanin ɓangarorin biyu ya kai wani mataki mai tsanani, inda suka yi ta musayar kalamai cikin ɗaga murya yayin wani taro da aka tashi baram-baram.

An gudanar da taron ne bayan tsofaffin jami’an sojin da ke zanga-zanga sun rufe babbar ƙofar shiga hedikwatar hukumar fansho saboda abin da suka bayyana a matsayin kuskuren lissafin kuɗaɗen fanshonsu da sauran haƙƙoƙinsu.

Masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanal Innocent Azubuike mai ritaya, sun isa wurin da yawansu tun da misalin ƙarfe 8:30 na safe, inda suka yi kira ga shugaban ƙasa da ya shiga tsakani domin warware matsalar.

Sun bayyana cewa sun ɗauki matakin ne bayan sun lura cewa hukumar na ƙoƙarin samar da bambance-bambance marasa muhimmanci a tsarin fansho da yadda ake biyan kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

An sauya shugaban hukumar fansho

Kwanaki bayan takaddamar, ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya guda. Wata majiya ta bayyana cewa lamarin ya kuma sa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, da Babban Hafsan Tsaron Najeriya suka ji ba dadi.

Sai dai bincike ya nuna cewa hukumomin soji sun cire Air Vice Marshal Mikail Abdulraheem na rundunar sojin saman Najeriya daga matsayin shugaban hukumar fanshon sojoji sakamakon abin da ya faru.

Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana rattaba hannu a fadarsa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ana zargin ya jawo abin kunya

Wani babban jami’in soji da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa ana sa ran AVM Abdulraheem zai ajiye mukaminsa tare da miƙa ragamar shugabancin hukumar ga wani mutum a ranar Laraba.

Wata majiya mai matsayi a cikin sojojin ta ce:

“Zanga-zangar da tsofaffin sojoji suka yi a makon da ya gabata ta jawa abin kunya ga fadar shugaban ƙasa da rundunonin soji, Ina ganin wannan ne dalilin da ya sa aka nemi shugaban hukumar ya ajiye mukaminsa.”

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

A halin da ake ciki, ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar, Squadron Leader Aliyu Mohammed, domin ya yi tsokaci a hukumance kan lamarin ba.

An fara biyan sojoji sabon albashi

Kun ji cewa jami’an sojojin Najeriya sun fara karɓar sabon albashin da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a watan Agustan da ya gabata.

Ƙarin albashin ya kasance tsakanin kashi 30 zuwa 80, gwargwadon matsayi, kuma ya shafi kusan jami’an tsaro 250,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262