Manyan Labarai A Yau
Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, John Kizito Bonzena, ya bukaci Gwamna Agbu Kefas ya waiwayi 'yan siyasa a jihar. Ya ce suna shan wahala.
Mutanen Rivers sun zargi NNPCL da amfani da tsohon mai a matsayin wanda aka tace a matatar Fatakwal. Mutanen sun ce an boye gaskiya ga yan Najeriya.
Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da Laftanar Janar, Olufemi Oluyede, a matsayin babban hafsan sojojin kasa (COAS). An tabbatar da shi ne bayan tantance shi.
Gwamnatin jihar Legas ta ci gaba da ɗaukar mataki mai tsauri kan masu taka dojar haramta hayaniya da ajiye kaya da kan ƙa'ida ba, ta rufe muhimman wurare.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana cewa fetur din da za a rika samarwa daga matatar Port Harcourt da ke Rivers, na gidajen man kamfanin ne kawai.
Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban babbar kotun tarayyya.
Wani jagoran jam'iyyar NNPP a yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Adebisi Olopoeyan, ya dauki matakin ficewa daga jam'iyyar. Ya ce ya yi hakan ne saboda wasu dalilai.
An samu tashin gobara a harabar ofishin gidan rediyon Najeriya da ke Legas. Jami'ai sun yi kokarin kashe gobarar wacce ba a san musababbin tashin ta ba.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da matarsa, Oluremi Tinubu sun isa birnin Farisa na ƙasar Faransa da yammacin jiya Laraba, sun fara ziyarar aiki ta kwana 3.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari