Sheikh Pakistan Ya Kama Tallar Tinubu Gadan Gadan, Ya Ce Ya Fi Buhari Kokari

Sheikh Pakistan Ya Kama Tallar Tinubu Gadan Gadan, Ya Ce Ya Fi Buhari Kokari

  • Tsohon shugaban hukumar NAHCON, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi gargadin cewa hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa'adi na biyu na iya jefa kasar cikin rikicin siyasa
  • Pakistan ya ce ya kamata a bar Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu domin tabbatar da adalci wajen sauya shugabanci tsakanin Arewa da Kudu
  • Ya bayyana cewa an samu saukin farashin kayan abinci da inganta tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a karkashin gwamnatin jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Sheikh Pakistan ya yi gargadin cewa hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu wa'adi na biyu na iya jefa Najeriya cikin rikicin siyasa a nan gaba.

Sheikh Pakistan ya yabi Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce Sheikh Pakistan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wasu kungiyoyin matasa a gidansa da ke Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu na da abin da zai fada wa yan Najeriya su zaɓe shi a 2027? Baba Ahmed ya yi magana

Meyasa Sheikh Pakistan ke son Tinubu ya zarce?

Ya ce ya kamata a bar Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu domin tabbatar da adalci wajen sauya shugabanci tsakanin Arewa da Kudu, kamar yadda aka bar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa'adi biyu a kan mulki.

Tsohon shugaban na NAHCON ya bayyana inganta tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma raguwar farashin kayan abinci a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatin jam'iyyar APC.

Ya kuma yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta gaji manyan matsalolin tsaro guda biyu, wato ta'addancin Boko Haram, wanda ya fara kafin mulkin Buhari, da kuma ayyukan 'yan bindiga, wadanda ya ce suka bulla a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar.

Pakistan ya yi bayani kan tsaro

"Idan ka duba matsalar rashin tsaro da wasu 'yan siyasa ke amfani da ita wajen yakin neman zabe, kafin Buhari ya zama shugaban kasa, babu satar mutane domin karbar kudin fansa. Ba a samun irin wadannan hare-hare a jihohin Zamfara, Kaduna, Sokoto da Kebbi ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba

"Satar mutane ta fara ne a lokacin mulkin Buhari. Tabbas, Buhari ya gaji ta'addancin Boko Haram, amma ayyukan 'yan bindiga sun fara ne a lokacin mulkinsa. Wannan yana nufin cewa Tinubu ya gaji manyan matsalolin tsaro guda biyu, wato satar mutane da ta'addancin Boko Haram." In ji shi.

Ya kara da cewa siyasar kabilanci ba za ta amfani Najeriya ba, yana mai gargadin cewa adawa da sake zaben Tinubu saboda yankin da ya fito na iya jawo matsala ga kasar.

Ya gargadi 'yan siyasa

Pakistan ya kara da cewa:

"Dole ne mu yi wa Tinubu adalci. Irin siyasar da muke yi, inda muke kin mutum saboda yankin da ya fito, tana da hadari. Idan muka ci gaba da haka, za mu sha wahala a nan gaba."
"Tinubu ya goyi bayan marigayi Muhammadu Buhari, ya kuma dage cewa ya kammala wa'adinsa biyu, duk da cewa yana fama da rashin lafiya. Amma yanzu wasu mutane suna kokarin hana Tinubu wa'adi na biyu. Wannan na iya jefa kasar cikin rikicin siyasa a nan gaba."
"Babu wanda zai bari wani dan Arewa ya yi wa'adi biyu."

Ya kwatanta tsaro a yanzu da baya

Pakistan ya ce a lokacin da Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu, tafiya daga Abuja zuwa Kaduna na iya jefa rayuwar matafiya cikin hadari.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Tinubu ya yi yabo ga ADC, ya fadi alherin da ta yi masa

Ya ce a wancan lokacin, matafiya kan samu natsuwa ne kawai idan sun isa Kaduna lafiya. Sai dai ya bayyana cewa a yanzu, mutum na iya tashi daga Abuja da karfe 12 na dare ya isa Kaduna lafiya. A cewarsa, wannan na nuna cewa an samu ci gaba a fannin tsaro.

Sheikh Pakistan ya tallata Tinubu
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan zaune a wurin taro Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Source: Twitter

Abin da za a tallata Tinubu da shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mayar da hankali kan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar a yaƙin neman zaɓen 2027

Sanata Yari ya ce za su nuna ayyuka maimakon yin zagi ko kai hare-hare na kashin kai kan ’yan takarar jam’iyyun adawa.

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng