Ana Wata ga Wata: Makinde Ya Fallasa Shirin Gwamnatin APC kan Jam'iyyun Adawa
- Seyi Makinde ya zargi APC da ƙoƙarin hana jam’iyyun adawa haɗa kai, yana mai cewa ya kamata al’ummar Kudu maso Kudu su kwato abin da ya kira ikon zaɓensu
- Gwamnan ya bayyana cewa yana da yakinin jam’iyyar APM za ta samu goyon bayan al’ummar yankin a zaɓe mai zuwa
- Makinde ya soki wasu manufofin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa shirye-shiryen CNG da da ɗanyen mai a Naira ba su kawo sauƙin sufuri ga ’yan Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Akwa Ibom - Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Injiniya Seyi Makinde, ya yi zargi kan jam'iyyar APC.
Gwamna Makinde ya zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ƙoƙarin murƙushe jam’iyyun adawa a Najeriya.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2026 yayin taron tattaunawa da jama’a na shirin neman shugabancin ƙasa na 2027 mai suna MakindeDaura 2027, wanda aka gudanar a Uyo, jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan
Jam'iyyun adawa 3 Sun haɗa kai da APC domin yallata Shugaba Tinubu, an jero sunayensu
Ya ce kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, APC ba ta da gagarumin tasiri a jihohin yankin Kudu maso Kudu, amma bayan zaɓen ta fara ƙoƙarin raunana sauran jam’iyyun siyasa.
Ya zargi APC da hana ’yan adawa haɗa kai
Gwamnan ya yi zargin cewa APC tana yin duk mai yiwuwa domin hana jam’iyyun adawa haɗa kai, amma ya ce yana da tabbacin za a iya sauya yanayin siyasa a yankin.
“Zan iya gaya muku cewa suna yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ’yan adawa ba su haɗa kai ba. Amma ina da saƙo a gare su; ina nan a yankin Kudu maso Kudu, kuma ina aiki da bayanai, tunani mai ma’ana da kimiyya.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa daga cikin jihohi shida na yankin Kudu maso Kudu, biyar ba sa ƙarƙashin APC kafin zaɓen 2023, amma a cewarsa, bayan zaɓen an karkatar da goyon bayan da jama’a suka bayar zuwa APC saboda tasirin gwamnatin tarayya.
“Daga cikin jihohi shida na wannan yanki, biyar ba sa ƙarƙashin APC. Washegari bayan zaɓen, an kwace wa’adin da kuka bayar da yardarku aka kai shi APC saboda wannan gwamnati. Yanzu kuna da damar kwato abin da yake naku. Ku gaya musu wanda ya mallaki wannan yanki.” In ji shi.
Ya ce APM za ta samu goyon bayan yankin
Makinde ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa al’ummar Kudu maso Kudu za su zaɓi jam’iyyar APM a zaɓe mai zuwa, kamar yadda ya ce ba su goyi bayan APC ba a zaɓen 2023.
“Ina da tabbaci dari bisa ɗari, har ma da ƙarin kashi ɗaya, cewa kamar yadda wannan yanki bai zaɓi APC ba a zaɓen 2023, haka za su zaɓi APM a zaɓe na gaba.” In ji shi.
Makinde ya soki manufofin gwamnatin Tinubu
Gwamnan ya kuma zargi gwamnatin tarayya da fara manyan ayyuka amma ta kasa kammala wasu daga cikinsu, yana mai cewa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suna ƙara wahalar da rayuwar ’yan Najeriya.
Makinde ya yi tambaya kan tasirin wasu shirye-shiryen gwamnati, musamman shirin amfani da iskar gas na CNG a motocin sufuri da kuma shirin sayar da ɗanyen mai a Naira.
“Ba za ku ci gaba da ƙara wa ’yan Najeriya wahalar rayuwa ba. Duk abin da suka yi, sai an ce babba ne. Suna son gina babbar hanyar mota ta musamman. Akwai shirin shugaban ƙasa na CNG, amma bai haifar da wani sakamako ba."
"Shirin sayar da ɗanyen mai a Naira ma bai haifar da wani sakamako ba. Shin waɗannan shirye-shiryen sun rage kuɗin sufuri ga miliyoyin ’yan Najeriya?” In ji shi.

Source: Facebook
Kuri'un da Makinde ya yi hasashen samu
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam’iyyarsa na shirin lashe zaben 2027 da gagarumin rinjaye.
Makinde ya ce APM na da burin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103 (kimamin kuri'u miliyan 68) da suka yi rajista.
Asali: Legit.ng

