Maiduguri
Hedikwatar tsaro ta ce ta mika mutane 313 da ta kama ga gwamnatin Borno bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri. An gane mutanen ba su da laifi.
Yayin da ake zargin shugaban sansanin Bama da ke jihar Borno, Abbah Tor da karkatar da wasu kayayyaki, Gwamna Zulum ya fatattake shi daga sansanin.
Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutum biyu, mace da namiji turmi da tabarya a cikin cocin ADC kwalejin ‘yan sanda da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Mutawali Shettima Bukar a matsayin sabon Wazirin Borno. Shehun Borno, Abubakar Elakanrmi ya mika sunan Bukar.
Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya umurci dukkanin ciyamomin kananan hukumomin jihar da su rinka sa hannu a na'urar shaidar zuwa aiki sau hudu a rana.
Rundunar Sojojin Najeriya ta yi ram da jami'inta da ake zargi da kisan wani direban babban mota a hanyar Gamboru-Dikwa. Ta sha alwashin hukunta shi.
Gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin kammala gina makarantun koyon addini da Larabci guda 27 a fadin jihar kafin saukar Gwamna Zulum. Akwai makarantu 8 a jihar.
Shugaba Bola Tinubu ya ja kunnen dakarun soji da su gujewa kai hare-hare kan fararen hula, inda ya sha alwashin yin bincike kan harin Kaduna don hukunta masu laifin.
Gobara a sanyin safiyar ranar Laraba ta yi sanadin mutuwar 'yan gudun hijira biyu tare da kona sama da gidaje 1,000, hukumar SEMA ta bayyana hakan.
Maiduguri
Samu kari