Borno: Gobara Ta Yi Barna a Sansanin ’Yan Gudun Hijira, Gidaje 1,000 Sun Kone, Mutane 2 Sun Mutu

Borno: Gobara Ta Yi Barna a Sansanin ’Yan Gudun Hijira, Gidaje 1,000 Sun Kone, Mutane 2 Sun Mutu

  • Wata gobara ta tashi da safiyar ranar Laraba a sansanin 'yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri, hukumar SEMA ta bayyana
  • Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar ta yi sanadin mutuwar 'yan gudun hijira biyu tare da kona sama da gidaje 1,000
  • Sai dai hukumar SEMA ta ce, tuni ta fara yin bincike kan lamarin, sannan ta samar da abinci da wasu kayayyaki ga wadanda abin ya shafa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Maiduguri, jihar Borno - Wasu ‘yan gudun hijira (IDP) guda biyu sun mutu, sannan sama da gidaje 1,000 sun kone kurmus, a wata mummunar gobara da ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar IGP da Rundunar ’Yan Sanda naira miliyan 200 kan garkame matar aure

Rahotanni sun bayyana cewa, gobarar ta fara ne da karfe shida na safiya, kuma ta dauki sama da awa guda kafin jami’an kashe gobara da hadin guiwar mutane su shawo kan ta.

Gobara a sansanin 'yan gudun hijira, Borno
Hukumar SEMA ta fara raba kayan tallafi ga wadanda gobarar ta shafa Hoto: TheGuardian
Asali: Twitter

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Dakta Barkindo Muhammad, ya sanar da hakan a ranar Laraba a Maiduguri, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar SEMA ta kai dauki sansanin Muna Alamdari

Ya ce, jami’an hadin gwiwa na farar hula, jami’an tsaro, da sauran mutane, su ka taru wajen kashe gobarar.

Muhammad ya ce, hukumar ta fara tantance irin barnar da gobarar ta yi, sannan ta yi kokari na bayar da agajin gaggawa ga wadanda iftila'in gobarar ya shafa.

“Mun samar da buhunan shinkafa 500, barguna da sauran abubuwan da ba na abinci ba domin rage musu radadin halin da suka shiga ,”

Kara karanta wannan

Mahara sun bukaci miliyan 53 kudin fansar malamin addini da wasu mutum 2 a jihar Arewa

A cewar Muhammad..

Gini ya rufta kan 'yan sansanin gudun hijira, 7 sun mutu

A wani labarin, akalla mutum bakwai ne yan gudun hijira suka riga mu gidan gaskiya lokacin da ginin wani ajin da ke dauke da su a wata makaranta ya rufto a karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, cewar rahoton Legit Hausa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa ajin wanda yake dauke da 'yan gudun hijirar masu yawa, ya rufto da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ranar Litinin, a dalilin ruwan sama kamar da kwarya da ya auku ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel