Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Shugaban NLC Ya Rasu a Watan Azumi

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Shugaban NLC Ya Rasu a Watan Azumi

  • Ali Chiroma, tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya ya rasu da yammacin ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024 a jihar Borno
  • Ɗan uwansa kuma sakataren ƙungiyar NUJ ta jihar Borno, Ali Ibrahim Chiroma, ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar
  • Marigayi Kwamared Ali Chiroma ya riƙe kujerar shugaban NLC daga 1984 zuwa 1988 lokacin da gwamnatin sojoji karkashin IBB ta rushe ƙungiyar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri, Jihar Borno - Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Ali Chiroma, ya riga mu gidan gaskiya.

Chiroma ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranar 2 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta ɗauki mataki kan ɗan Kwankwaso da mutum 3 da Gwamna Yusuf ya naɗa

An fara jimamin rasuwar Ali Chiroma.
An yi amfani da wannan hoton ne domin nuni kawai amma wanda ke jiki ba shi da alaƙa da labarin Hoto: Ijubaphoto
Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, ɗaya daga cikin dangin mamacin, wanda ke riƙe da kujerar sakataren ƙungiyar ƴan jarida (NUJ) reshen jihar Borno, Ali Ibrahim Chiroma ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwayar jaridar Vanguard, wani sashin sanarwan ya ce:

"Cikin jimami da alhini muke sanar da rasuwar Kwamared Ali Chiroma, tsohon shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC).
"Ya cika ne da yammacin nan (ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024) a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UNIMAID)."

Wani lokaci ya shugabanci ƙungiyar NLC?

Legit Hausa ta tattaro cewa marigayi Ali Chiroma ya riƙe kujerar shugaban ƙungiyar kwadago NLC ta ƙasa daga shekarar 1984 zuwa 1888.

Sai dai ya bar muƙamin bisa dole lokacin da Gwamnatin Sojoji karkashin jagorancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya rushe kungiyar gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai sake fita daga Najeriya zuwa ƙasar waje a watan azumi, bayanai sun fito

Yadda mataimakin kwamishina ya yi ajalin kansa

A wani rahoton na daban kun ji cewa mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Gbolahan Oyedemi ya halaka kansa a cikin gidansa da ke garin Ogbomoso, jihar Oyo.

An rahoto ceqa Oyedemi wanda tsohon dogarin tsohon gwamnan Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala ne, ya yi ajalin kansa ta hanyar rataya a gidansa da ke Ogbomoso

Wata majiya daga iyalan mamacin, ta yi bayanin cewa mataimakin kwamishinan ya ziyarci Ogbomoso ne domin bikin Easter amma daga bisani akan tsinci gawarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel