Zulum Ya Fatattaki Shugaban Sansanin ’Yan Gudun Hijira Kan Wasu Zarge-Zarge, Bayanai Sun Fito

Zulum Ya Fatattaki Shugaban Sansanin ’Yan Gudun Hijira Kan Wasu Zarge-Zarge, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake zargin shugaban sansanin Bama da ke jihar Borno da karkatar da wasu kayayyaki, Gwamna Zulum ya sallame shi
  • Zulum ya kori Abbah Tor daga cikin sansanin ‘yan gudun hijirar bayan da ya kai ziyara lokacin raba kayayyaki a sansanin
  • Wani mai suna Umar daga hukumar UNICEF shi ne ya hada baki da Tor wanda kuma shi ne shugaban SEMA don karkatar da kayan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno – Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sallami shugaban hukumar SEMA, Abbah Tor.

Gwamnan ya sallami Tor ne kan zargin hannu a karkatar da wasu kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bama a jihar Borno.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kashe kasurgumin dan bindiga a Arewa, sun kwato muggan makamai

Zulum ya sallami shugaban sansanin gudun hijira kan wasu dalilai
Gwamna Zulum ya kori shugaban sansanin 'yan gudun hijira kan karkatar da kaya. Hoto: Babagana Zulum.
Asali: Facebook

Wane mataki Zulum ya dauka?

Gwamnan ya kori Abbah daga cikin sansanin ‘yan gudun hijirar yayin da ya kai ziyara lokacin raba kayayyaki, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya sanar da ‘yan gudun hijirar cewa Abbah shi ke sace musu kayayyaki tuntuni inda ya umarce shi da kada ya dawo sansanin.

ZagazolaMakama ya ruwairo yadda wasu daga cikin jami’an sansanin a Bama suka sace tankokin ruwa akalla 30 da kuma wasu karafuna.

Ta yaya lamarin ya faru?

Tun farko wani mai suna Umar, ma’aikacin UNICEF ya hada baki da Ali Mala da ke hukumar RUWASA inda suka samu Abbah Tor don karkatar da wasu kayayyaki a sansanin.

Toh da wani Bakura Shettima sun amince da bukatar Umar duk da daya daga cikin ma'aikatan bai amince ba.

Umar ya ce an turo shi ne daga UNICEF don binciken bohula da duba wadanda basu ba da ruwa inda aka tabbatar masa uku daga ciki basu ba da ruwa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

Ya ce musu za a dauki tankokin ruwa 30 da wasu karafuna zuwa makarantar firamare ta Bama da kuma Maiduguri yayin da za a siyar da wasu don biyan kudin motar kayan.

Zulum zai samar da fetur mai sauki ga manoma

A baya, kun ji cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno zai rage farashin fetur ga manoma a jihar.

Zulum ya dauki wannan mataki ne ganin yadda tsadar fetur din ke hana inganta harkokin noma a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel