An Kama Soja Boye da Makamai Cikin Buhun Shinkafa a Jihar Borno

An Kama Soja Boye da Makamai Cikin Buhun Shinkafa a Jihar Borno

  • Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cafke wani soja mai suna Mubarak Yakubu dauke da makamai cikin buhu a jihar Borno
  • Jami'in yada labaran rundunar ne, Onyema Nwachukwu ya bayyanawa manema labarai a jiya Alhamis, 09 ga watan Mayu
  • Janar Nwachukwu ya tabbatar da cewa yanzu haka rundunar tana tsare da sojan tare da bayyana irin matakan da suke dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kama wani soja mai suna Mubarak Yakubu boye da makamai cikin buhun shinkafa.

Nigerian Army
Rundunar sojin Najeriya ta kama jami'inta da ya boye makamai a Borno. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Makaman da aka kama sojan da su

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama sojan ne dauke da harsashi 756 da gurneti 36 a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu a sanadiyyar hatsarin iskar gas a jihar Lagos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama sojan ne dauke da makamai ba bisa ka'ida ba a lokacin wani bincike da rundunar ta yi a Maiduguri.

Jawabin kakakin rundunar sojan Najeriya

Jami'in yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyemema Nwachukwu ya zanta da manema labarai kan lamarin a jiya Alhamis.

Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da cewa yanzu haka ana tsare da Mubarak Yakubu domin gudanar da bincike.

Birgediya Janar din ya ce za a zurfafa bincike domin gano dalilan da suka sa shi daukan makaman da kuma abin da zai aikata da su, cewar jaridar Vanguard.

Jami'in ya kara tabbatar da cewa da zarar sakamakon bincike ya bayyana rundunar za ta dauki matakin da ya dace kan sojan.

Yabo ga wadanda suka kama shi

Har ila yau ya mika godiyar rundunar ga wadanda da suka cafke shi wurin kokarin su na tabbatar da aikin su na tafiya kan ka'ida.

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Ma'aikatar tsaro ta rabawa sojoji sababbin motocin yaki masu sulke

A karshe ya ce rundunar za ta cigaba da gudanar da aiki bisa tsari da doka wurin samar da tsaro a kasa baki daya.

Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bingiga haye akan rakuma da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutum 11 da ke sana'ar itace a Borno.

Lamarin wanda ya faru a yammacin ranar Litinin, rahotanni sun nuna cewa an yi wa mutanen su 11 yankan rago a lokacin da suke aikin itace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel