‘Yan Sanda Sun Kama Mace da Namiji Turmi da Tabarya a Wajen Bauta a Jihar Arewa

‘Yan Sanda Sun Kama Mace da Namiji Turmi da Tabarya a Wajen Bauta a Jihar Arewa

  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Borno sun kama wasu mutum biyu (mace da namiji) kan sheke aya a cikin coci
  • Majiyoyi sun ce an kama masu laifin ne turmi da tabarya da misalin karfe 11:40 na safiyar Litinin, 12 ga watan Fabrairu
  • Limamin cocin, Danjuma Adamu ya fada ma 'yan sanda cewa bayan faruwar lamarin, Khadija ta ce Kaka Ali ya biya ta N1,000 domin tarawa da ita a takaice

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Maiduguri, jihar Borno - Jami'an 'yan sanda sun kama wasu mutum biyu (mace da namiji) kan yin sharholi ta kwanciya a cikin cocin ADC kwalejin 'yan sanda a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, majiyoyi sun ce an kama Kaka Ali Umar na hanyar Damboa da Khadija Adam ta yankin Ngomari Maiduguri turmi da tabarya da misalin karfe 11:40 na safiyar ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu.

An kama mace da namiji suna tarawa a cikin coci
‘Yan Sanda Sun Kama Mace da Namiji Turmi da Tabarya a Wajen Bauta a Jihar Arewa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An yi zargin wani jami’in tsaro da ke aiki a Cocin (an sakaya sunansa) ne ya taimaka wa wadanda ake zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama mace da namiji turmi da tabarya a coci

Limamin cocin, Danjuma Adamu, ya fada ma tawagar 'yan sanda da ke gudanar da bincike cewa an kama wadanda ake zargin ne turmi da tabarya a cikin cocinsa.

Malamin addinin ya fada ma 'yan sanda cewa "bayan lamarin, Khadija ta ce Kaka Ali ya biya ta N1,000 domin tarawa da ita a takaice".

Wata majiya ta kusa da tsaro, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ana gudanar da bincike kan mutanen biyu a ofishin 'yan sanda na Metro, rahoton LIB.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Majiyar ta ce bayan nan za a tura lamarin zuwa hukumomin da suka kamata don ci gaba da bincike da yanke hukunci.

An kama dalibai suna lalata a kungiyance

A wani labarin, mun ji cewa an dauki mummunan mataki kan wasu daliban babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe su 20 saboda lalata da juna a watan Yuli.

An kama daliban haihuwar ioyayensu suna lalata yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel