Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro

Borno: Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Sake Daukar Makamai, Sun Farmkaki Jami’an Tsaro

  • Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro ya ruwaito cewa tubabbun 'yan Boko Haram sun farmaki jami'an tsari a Borno
  • Makama, ya ce lamarin ya faru a ranar Laraba inda wadanda ake zargin suka kona shingayen bincike na hukumar NDLEA da NCS
  • Jim kadan bayan kona shingayen ne Makama ya ce 'yan ta'addan suka farmaki ofishin rundunar 'yan sanda na Kasuwar Fara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Borno - Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne da suka tuba sun sake daukar makamai yayin da suka farmaki jami'an tsaro a jihar Borno.

Mayakan Boko Haram sun farmaki jami'an tsaro a Borno
Tubabbun mayakan Boko Haram sun kona shingen binciken jami'an tsaro a jihar Borno. Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

An ruwaito cewa sun kona shingayen binciken kwakwaf na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da hukumar kwastam ta Najeriya (NCS).

Kara karanta wannan

"Sako ga masarautar Zamfara": 'Yan bindiga sun saki bidiyon hadimin sarki da suka sace

'Yan Boko Haram sun farmaki jami'an tsaro

Zagazola Makama, wani mai sharhi kan al'amuran ta'addanci a yankin tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya rahoto cewa tubabbun 'yan Boko Haram din sanye da kakin sojoji sun mamaye Kasuwar Fara a Maiduguri inda suka fatattaki jami'an hukumomin.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kona dukkanin shingen binciken, inda suka koma ofishin ‘yan sanda reshen Kasuwar Fara da yunkurin sakin mambobinsu takwas da ke tsare.

'Yan sanda sun yi artabu da mayakan

Makama ya ce an kama wadanda ake tsare da su ne a ranar 24 ga watan Afrilu yayin wani samame da ‘yan sanda suka kai a wani kauye mai suna Kasuwan Fara, in ji jaridar The Cable.

Mai fashin bakin ya ce jami’an ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa an fi karfin ‘yan ta’addan lamarin da ya tilasta su guduwa daga wurin.

Kara karanta wannan

Kano: Dilan wiwi da 'yan sanda ke nema ruwa a jallo ya shiga hannu

Ya ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo maharan.

Kudin fansho: Ma'aikata a Borno sun koka

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa ma'aikata a jihar Borno sun koka kan Naira 4,000 da wasu tsofaffin ma'aikata ke karba a matsayin kudin fansho a wata.

Kungiyar kwadago reshen jihar yayin da take rokon Gwamna Babagana Zulum da ya duba lamarin ta yi nuni da cewa babu abin da kudin za yi a wannan yanayin na tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.