Tinubu Ya Gargadi Sojojin Najeriya: “Kar Ku Kuskura Ku Kara Jefa Bam Kan Fararen Hula”

Tinubu Ya Gargadi Sojojin Najeriya: “Kar Ku Kuskura Ku Kara Jefa Bam Kan Fararen Hula”

  • Shugaba Bola Tinubu ya ja kunnen dakarun soji da su gujewa kai hare-hare kan fararen hula, inda ya kara jajantawa al'ummar Kaduna
  • Tinubu wanda ya sha alwashin yin bincike kan harin garin Tudun Biri, ya kuma jinjinawa sojoji kan nasarar da suke samu a yaki da 'yan ta'adda
  • Ya kuma gargadi sojojin da su gujewa kai farmaki ga sauran hukumomin tsaro, kamar yadda ta faru tsakaninsu da 'yan sanda a jihar Adamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin ya gargadi sojojin Najeriya da su kauracewa jefa bam kan fararen hula, ya ce irin hakan ba za ta sake faruwa ba.

Kara karanta wannan

Sun yi mutuwar shahada, Tinubu ya magantu kan harin bam a Kaduna, ya fadi abu 1 da ya fi damunsa

Tinubu na martani ne kan harin bam din sojoji a Tudun Biri, jihar Kaduna, wanda ya kashe sama da mutum 100 masu maulidi tare da jikka wasu da dama.

Bola Ahmed Tinubu/Shuban kasa/Sojojin Najeriya
Shugaba Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya da su kauracewa jefa bam kan fararen hula. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ya yi wannan gargadin ne a Maiduguri a yayin bikin bude taron hukumar tsaro ta rundunar soji na shekarar 2023, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma kara tabbatar da umurtar hukumomin da abin ya shafa da su zage damtse wajen gano yadda abin ya faru tare da daukar matakin da ya dace.

Tinubu ya gargadi sojoji kan farmakar kawayen su

Ya ce:

"Hakika wannan babbar waki'a ce ga Najeriya, muna zubar da hawaye kan mutanen da aka rasa, maza da mata har da kananan yara.
"Za mu tabbatar an yi bincike kan lamarin tare da dakile hakan daga faruwa, wannan ne ya zama wajibi a gare ku, a kiyaye faruwar hakan."

Kara karanta wannan

"Mun fada mugun hannu": Sheikh Yabo ya caccaki gwamnatin Tinubu kan kisan masu maulidi a Kaduna

Ya ce dakarun soji na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda, yayin da aka dawo da zaman lafiya, ana samun farfadowar tattalin arziki.

Tinubu ya kuma bukaci dakarun sojin da su guje wa kai farmaki ga sauran hukumomin tsaro, biyo bayan musayar wutar da aka samu tsakanin sojoji da 'yan sanda a jihar Adamawa.

Yan bindiga sun haka mutum 4 a jihar Plateau

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai garin Dungwel da ke karamar hukumar Mangu, jihar Plateau.

Bayan kashe mutanen, an ruwaito 'yan bindigar sun kone gidan sarkin garin da iyalinsa a ciki, sai dai sojoji sun yi nasarar kubutar da su daga cikin gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel