Borno: Zulum Ya Dauki Wani Babban Mataki Kan Ciyamomin Da Ba Su Zuwa Aiki

Borno: Zulum Ya Dauki Wani Babban Mataki Kan Ciyamomin Da Ba Su Zuwa Aiki

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bullo da sabon tsarin yi wa ciyamomi rijistar zuwa aiki
  • A cewar Zulum, kowanne ciyaman zai rinka shigar da shaidar yana wajen aiki sau hudu a rana
  • Gwamnan ya ce ya bullo da wannan tsarin ne la'akari da yadda wasu ciyamomi ke bijirewa zuwa aiki da gangan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya umurci dukkanin ciyamomin kananan hukumomin jihar da su rinka sa hannu a na'urar shaidar zuwa aiki sau hudu a rana.

Zulum ya bayar da wannan umurnin a ranar Litinin a Maiduguri, babban birnin jihar, a taron rantsar da zababbun ciyamomin 27 na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya cire tsoro, ya faɗi abu 1 da ƴan Najeriya zasu yi su samu sauƙi da ci gaba

Ciyamomi a Borno za su rinka sanya hannu kan rijistar halartar aiki sau hudu a rana, in ji Zulum
Ciyamomi a Borno za su rinka sanya hannu kan rijistar halartar aiki sau hudu a rana, in ji Zulum. Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Gwamnan ya ba ma'aikatar kananan hukumomi umurnin samar da na'urar 'biometric' don ba ciyamomin damar shigar da rahoton zuwan su aiki da karfe 8 na safe, 12 na rana, 2 na rana da 3:30 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Zulum ya ce game da rijistar zuwa aikin ciyamomi

Zulum ya ce wannan matakin zai dakile ciyamomin da ke fashin zuwa aiki ba tare da wani dalili ba, inda ya ce rashin zuwa aiki na iya sa a tsige ma'aikaci.

Ya ce:

"Mun shawarci ciyamomi, ba sau daya ba, amma ba sa daukar shawarar mu,"

The Cable ta ruwaito gwamnan na ci gaba da cewa:

"Yanzu mun samar da hanyar da za ta tabbatar da cewa ciyamomin sun je aiki, wanda ke da matuƙar amfani."

Abubuwan da Zulum ke nema daga ciyamomin jihar Borno

Kara karanta wannan

"Ku tuba ko a sheke ku": Wike ya gargadi masu garkuwa da mutane da masu yi masu leken asiri

Zulum ya yi nuni da cewa yanzu an samu tsaro sosai a jihar, don haka dole ciyamomi su ba shi hadin kai don farfado da jihar da taimakawa 'yan gudun hijira.

Ya kuma bukaci ciyamomin da su kasance masu alkinta dukiyar jihar, yayin da ya nemi su fadada ayyukansu lungu da sakunan yankunan su.

Zulum ya kuma karfafe su da su yi aiki tare da jami'an tsaro wajen wanzar da zaman lafiya da dawo da hukumar fararen huluna a yankin na su.

Gwamna Radda: Mutane su kare kansu daga 'yan bindiga

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda, ya bukaci al'ummar jiharsa da su tashi su kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Gwamna Radda ya ce gwamnatin sa za ta ba al'ummar jihar duk wani gudunmawa da suke bukata don aiwatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel