Jihar Legas
Tsohon darakta janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a inuwar Labour Party, Doyin Okupe, ya fito daga hannun jami'an hukumar EFCC bayan DSS ta kama shi.
Shugaban jam'iyyar Labour Partya watu LP na jihar Legas, Kayode Salako, ya sauka daga kan kujerarsa, yace zai maida hankali kan takarar majalisa da ya ke nema.
Ndubisi Uwadiegwu, wani magidanci dan asalin Jihar Enugu ya halaka matsarsa Ogochukwu Enene da duka saboda biredi a Legas. Ta ce ya siya musu biredi ya ki siya.
Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta yi All-wadai da yadda wani direba ya banke jami'inta, ya ji masa mummunan rauni ya yi fecewarsa a kan wata gadar jihar.
An nadi bidiyon wani gurgu nakasasshe a jihar Legas yayinda ya mayar da 'yar kekensa wata kwaryakwaryar shagon sayar da kayan furovishon babu ruwansa da bara.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jaddada cewa duk wanda ba shi da katin zabe ba samu damar jefa kuri'a ba a zabe mai zuwa, tace an barta da PVC da yawa.
Foluke Abosede Ntukdem, tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya ta riga mu gidan gaskiya. Ta rasu a gidanta Legas a cikin barcinta kamar yadda danta ya tabbatar.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas da Ogun sun tabbatar da tashin wata gobarar cikin dare a fitacciyar kasuwar Ajimula dake tsakanin iyakokin Ogun da Legas.
Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda, PSC, ta amince da dakatar da ‘Dan sandan da ake zargi da bindige lauya Bolanle Raheem a ranar Kirsimeti a jiharr Legas.
Jihar Legas
Samu kari