Da Dai In Ci Amanar Magoya Bayana, Gara in Mutu, Peter Obi

Da Dai In Ci Amanar Magoya Bayana, Gara in Mutu, Peter Obi

  • Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP, ya bayyana cewa gara ya mutu da dai ya ci amana ko ya gazawa magoya bayansa
  • Obi ya sanar da cewa kalubale da kasar nan ke fuskanta zai zama tarihi matukar an samu shugabanci nagari, kuma shi zai iya jagorancin da ya dace
  • Yace dole ne laifuka su yawaita a kasar nan ganin cewa talauci yayi katutu ga jama’a, don haka zai assasa noma wanda zai ciyar da ‘yan kasa

Legas - ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, a ranar Litinin a Legas yace gara ya mutu da dai ya ci amanar magoya bayansa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Peter Obi
Da Dai In Ci Amanar Magoya Bayana, Gara in Mutu, Peter Obi. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Obi ya kara da cewa shugabanci nagari zai kawo karshen dukkan kalubalen da suka addabi kasar nan, jarida Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwankwaso Bashi da Karfi Yanzu, Ba zai Kai Labari ba a 2023

Obi ya sanar da hakan ne a taron zauren editoci.

Najeriya na cikin manyan kalubale, Obi

Tsohon Gwamnan jihar Anambra yace kasar na cikin kalubale masu tarin yawa saboda ci take kawai bata iya samar da komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda yace, idan kasa tana samar da abubuwan bukata, kashi uku cikin hudu na kalubalenta zasu yi kaura.

TheCable ta rahoto, ya lissafo kalubalen da ke damun Najeriya da suka hada da rashin aikin yi, talauci, laifuka da rashin tsaro.

“Ba za a ce yawan jama’a haka suna rayuwa cikin tsananin talauci ba kuma a rasa laifuka da sauransu ba.”

- Yace.

Noma zamu koma, mu bar nan fetur, Obi

Yace Najeriya tana da kasa mai kyau kuma hakan zai matukar amfani wurin samar da kayayyaki da suka shafi noma.

“Burin kasar nan da makomarta shi ne wannan filin da muke kin nomawa, ba wannan man fetur din da kuke gani ba.

Kara karanta wannan

Mun tuba: PDP ta tafka kura-kurai daga 1999 zuwa 2015, Atiku zai gyara komai

“Abinda zan mayar da hankali a kai shi ne, saka ‘yan Najeriya kan hanyar samar da abubuwan bukata.
“Ba zai yuwu ba a ce ba zamu iya ciyar da kanmu ba.
“Dole ne mu dawo da martabar kasar nan, abinda hakan ke bukata kawai shi ne shugabanci da ya gane kuma zai iya gyara tsarin. Zan iya hakan.”

- Yace.

Waye ya dauka nauyin kamfen din Obi?

A bangaren daukar nauyin kamfen din shi, Obi yace akasin yadda ake hasashe ne, babu wanda ya dauka nauyin yakin neman zabensa.

Ya kara da cewa bai ba kowa kudi ba don ya janye masa ko ya tsaya masa.

Ganduje: Takarar Obi Atiku kadai zata gurgunta

A wani labari na daban, Gwamna Ganduje na jihar Kano yace takarar Peter Obi PDP kawai zata nakasa amma ba APC ba.

Yace ko a zaben 2019, kudu maso gabas bata zabi APC ba, PDP suka dinga zabe, don haka wasu kuri’un PDP ne LP zata zuga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel