Likitoci Sun Bayyana Abin Da Ya Haddasa Mutuwar Dan Davido, Ifeanyi

Likitoci Sun Bayyana Abin Da Ya Haddasa Mutuwar Dan Davido, Ifeanyi

  • Binciken da likitoci suka yi kan gawar dan Davido da matar da zai aure, Chioma Rowland ya nuna sakamakon mutuwarsa
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a wani rahoto a ranar 5 ga watan Nuwamba
  • Masu amfani da dandalin sada zumunta da dama sun yi martani da tambayoyi kan dalilin da zai sa dan shekara uku ya shiga ruwa

Legas - Rundunar yan sandan jihar Legas a ranar Asabar ta ce binciken da aka yi kan gawar Ifeanyi Adeleke, dan Davido da wacce zai aura, Chioma Rowland ya nuna cewa nutsewa a ruwa ne sanadin mutuwarsa.

Kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan cikin hira da ya yi da wakilin The Punch.

Kara karanta wannan

Kebera yake sha? Bidiyon mataccen takalmin da wani ya saka ya je neman aure ya ba mamaki

Davido da Ifeanyi
Likitoci Sun Bayyana Abin Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Dan Davido, Ifeanyi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hundeyin ya ce:

"An kammala binciken gawar. Ya tabbatar da cewa yaron (Ifeanyi) nutsewa ya yi."

Wata majiya, wacce ta tabbatar da lamarin ta ce dama yan sanda suna yin binciken gawa a irin wannan yanayin, sai dai idan iyalan mamaci sun ce ba su son ayi.

Majiyar ta ce:

"Duk da cewa iyalan har yanzu ba su ce komai ba saboda suna cikin juyayin rashi amma idan ba a ce kada a yi ba, tsarin da aka saba amfani da shi shi ne yin binciken da aka yi, kuma za mu bi wannan tsari kamar yadda muke yi a duk irin wannan yanayin mutuwa."

Majiyar ta cigaba da cewa yan sanda suna yi wa masu hidama su takwas na gidan Davido tambayoyi game da rasuwar Ifeanyi.

A lokacin wallafa wannan labarin, mai kula da yaron da mai girki suna tsare wurin yan sanda.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dura kan manoma, suna shirin kakaba musu haraji

Masu amfani da dandalin sada zumunta sunyi martani kan Ifeanyi Adeleke

tinie.temper:

"A cigaba da tsare su dai har sai sunyi bayani abin da yasa suka bari ya fita da yadda ya bude kofar."

vendorsinlagosng:

"Baby Ify yana tare da mala'iku."

seun_dreams:

"Bude jikin wannan yaron da sunan binciken gawa wani babban abin karya zuciya ne."

kofoworolabam:

"Ya kamata yan sanda sun tambaya a basu bidiyo!"

thesmartphonegirl:

"Wane ya bude kofar har yaron ya fita ya shiga wurin ninkayan su duba bidiyon cctv yanzu, ganin labarin nan abin bakin ciki ne."

Ifeanyi: Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Mawaki Davido Gaba Daya Kan Mutuwar Dansa

Rahotanni sun kawo cewa yan sanda sun kama dukkanin ma’aikatan gidan shahararren mawakin Najeriya, Davido kan mutuwar dansa, Ifeanyi.

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da cewar dukkanin ma’aikatan na tsare a hannunsu don amsa tambayoyi, Sahara Reporters ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel