Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30

Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30

  • Gawurtaccen ‘dan kasuwa kuma hamshakin maI arziki a Najeriya, Femi Otedola, ya nuna tsabar kauna ga diyarsa Florence Otedola wacce aka fi sani da DJ Cuppy yayin zagayowar ranar haihuwarta
  • Fitaccen ‘dan kasuwan man fetur din ya gwangwaje diyarsa da kyautar gida mai kimar £5,000,000 wanda yayi daidai da N2.6 biliyan a kudin Najeriya da ta cika shekaru 30
  • Hamshakin mai dukiyar ya sanar da diyarsa cewa ba zai taba mantawa da ranar haihuwarta ba kuma a koda yaushe yana matukar alfahari da ita

Legas - Biloniyan ‘dan kasuwan Najeriya, Femi Otedola, ya girgiza diyarsa Florence wacce aka fi sani da DJ Cuppy bayan ya gwangwaje ta da kyautar gida mai kimar £5,000,000 wanda yayi daidai da N2.6 biliyan a kudin Najeriya, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma, Yadda Wata Budurwa Ta Fada Tekun Lagas Akan Saurayi

DJ Cuppy at 30
Biloniya Otedola Ya Gwangwaje Diyarsa da Kyautar Gidan N2.6bn Yayin da ta Cika Shekaru 30. Hoto daga @cuppymusic
Asali: Twitter

Fitacciyar diyarsa ta cika shekaru 30 a duniya a ranar Juma’a, ta bayyana kyautar da ta samu daga mahaifinta inda ta fitar da hirar da suka yi da biloniyan ‘dan kasuwan.

Ina alfahari dake diyata, Otedola

A hirar da suka yi, Cuppy ta zargi mahaifinta da mantawa da ranar da ta cika shekaru 30 a duniya wanda yayi martani da cewa hakan ba zai taba faruwa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da sanar mata cewa, ya umarci wani mai suna Andy a bankin Barclay da ya siya mata gida mai kimar £5,000,000.

Hakazalika, biloniya Otedola ya bayyana cewa ba zai iya tunanin wata kyauta da ta dace ya bata ba saboda a koda yaushe yana alfahari da ita.

Wani ya bani kyautar Rolex, Cuppy

A daya bangaren, Cuppy ta je shafinta na Twitter inda ta bayar da labarin wani matashi da baya birgeta amma ya siya mata kyauta mai tsada domin murnar ranar zagayowar haihuwarta.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Yi wa Sarki Charles III da Matarsa Ihun Bama so tare da Jifansu da Kwai a Ingila

Ta rubuta:

“Wannan gayen ya siya min agogo Rolex kuma har yanzu bani da lokacin shi.”

Femi Otedola ya cika shekaru 60 a duniya

Legit.ng ta rahoto muku cewa fitaccen ‘dan kasuwar mai Femi Otedola ya cika shekaru 60 a duniya inda ya fitar da zunzurutun kudi yayi hayar jirgin ruwa.

Shi, iyalansa da abokan arziki zasu kwashe makonni uku suna zagaye da yawon shakqara a jirgin ruwan duk a cikin shagalin zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel