NDLEA Ta Damke ‘Yan Fakistan Dauke da Hodar Iblis a Filin Jirgin Sama na Legas

NDLEA Ta Damke ‘Yan Fakistan Dauke da Hodar Iblis a Filin Jirgin Sama na Legas

  • Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta tabbatar da kama wasu ‘yan kasar Fakistan biyu kan zargin safarar miyagun kwayoyi
  • ‘Yan kasar Fakistan din masu suna Asif Muhammad da Hussain Naveed an kama su da hodar iblis boye a amsa kuwa yayin da suka ce su ‘yan kasuwa ne
  • Har ila Yau, an kama wata budurwa mai suna Olufunmilayo mai shekaru 32 da hodar iblis, wiwi, Tramadol da Rohyphnol duk a Legas din

Legas - Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA ta damke wasu ‘yan kasuwar Fakistan a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas dauke da kilogiram 8 na hodar iblis.

Fakistani
NDLEA Ta Damke ‘Yan Fakistan Dauke da Hodar Iblis a Filin Jirgin Sama na Legas. Hoto daga @ndleanigeria
Asali: Twitter

Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar NDLEA yace an boye miyagun kwayoyin ne a amsa kuwwa wacce wanda ake zargin yake kokarin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Lahole, Fakistan ta Doha.

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Ciwan Kai Ga Atiku, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Samun Gagarumin Goyon Baya Daga Wasu Jiga-Jigan PDP

Yace mutum biyun da ake zargin sune Asif Muhammad da Hussain Naveed wadanda ke da katin zaman Najeriya kuma sun saba zuwa Najeriya kan kasuwancin tufafi.

Kamar yadda yace, an kama su a ranar Asabar a filin jirgin sama na Legas, kasa da mako daya bayan zuwansu Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daya bangaren, jami’an NDLEA dake Skyway Aviation Handling Company a ranar Juma’a sun kwace katan 13 na Tramadol 225mg da 200mg da aka shigo dasu daga Karachi, Fakistan.

Babafemi yace kayan suna da nauyin 465.10kg da 642,800 kwayoyi.

“A ranar da ta gabata, jami’an dake sashen NAHCO sun kama wasu miyagun kwayoyi kala-kala.”

- Yace.

An kama Budurwa da Kwayoyi a Takalma

“Wannan ya hada da wiwi, hodar iblis, kwayar Methamphetamine tare da Tramadol 225mg da Rohyphnol boye a takalma da fakitin sabulu da za a kai UAE, Dubai.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

“An kama wata budurwa mai shekaru 32 mai suna Oladitan Serah Olufunmilayo da kayan zata fitar da su.“

- Ya bayyana.

NDLEA a cikin watannin nan yana cigaba da tsanantawa a bangaren yaki da fataucin miyagun kwayoyi kuma ana samun nasarori.

Hukumar NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Miliyan 2.3 da Aka Shirya Kawo Wa Arewa

A wani labari na daban, NDLEA, hukuma mai yaki da shia da safarar miyagun kwayoyi ta kame tarin miyagun kwayoyi na opioids da sauran kayan buguwa da suka haura miliyan 2.3 da aka nufi kai wa jihohin Arewa.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin hukumar, Femi Babafemi a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi 22 ga watan Agusta, Channels Tv ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, jihohin da za a kai kayayyakin su ne kamar haka: Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe, da Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel