Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023

Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya fadama al’ummar Hausa-Fulani a jihar Lagas cewa Tinubu arewa za ta yi a zaben shugaban kasa
  • Ganduje ya kuma bayyana cewa jiharsa ta Kano za ta tarawa Bola Tinubu kuri’u fiye da ko’ina a Najeriya
  • Gwamnan wanda ya samu rakiyar Shettima da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu ya bukaci yan Legas da su yiwa yan takarar APC ruwan kuri’u a 2023

Lagos - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar Kano da su marawa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima baya a zaben 2023.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin wata ziyara da ya kaiwa al’ummar arewa a Alaba Rago da ke yankin Ojo na jihar, jaridar Punch ta rahoto. Ya kuma samu rakiyar Shettima da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu.

Ganduje
Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023 Hoto: Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Ganduje ya ce:

“Mun zo nan yau da tarin alkhairi kuma mun kawo maku labari mai dadi. Idan dai a arewacin kasar nan ne, batun shugabancin Tinubu ya dade da kammala. Muna jiranku ku mazauna Lagas don ku fito sannan marawa wannan baya da kuri’unku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A Kano, Asiwaju zai samu kuri’u fiye da wanda kowace jaha zata bashi.”

A nashi jawabin, Shettima ya bayyana cewa zaben 2023 lokaci ne da za a sakawa Tinubu a arewa, duba ga cewar ya marawa yan takara daga arewa baya a zabukan kasar na baya, rahoton TheCable.

“Ina son sanar da ku muhimmanci zabe na gaba. Ga mu da muka fito daga arewa, wannan lokacin rama alkhairi ne. A zabukan baya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya marawa yan takarar arewa baya don zama Shugaban kasar Najeriya a zaben fidda gwani na 2014 da 2015 kuma a zabukan baya, ba don tarin kuri’u da Asiwaju ya tara daga kudu maso yamma ba da Shugaba Buhari bai samu shugabancin APC ba.

“An maimaita irin haka a zaben 2019, yanzu lokacin biyan bashi ne. Mu mutane masu karamci ne, mu karrama alkawari da jajircewarmu sannan abu mafi muhimmanci muna so ku zabi APC. A zaben gwamna, Ina so ku fito ku zabi Babajide Sanwo-Olu.”

Dan takarar mataimakin Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa Tinubu ya sadaukar da kudirinsa sannan ya baiwa yan arewa ciki harda dan takarar PDP, Atiku Abubakar da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu dama.

A nasa martanin, Shugaban yan arewa a Lagas, Alhaji Yusuf Badaru, ya ce Hausawan Lagas na tare da APC kuma za su ribanya kokarinsu don tabbatar da ganin an zabi yan takarar jam’iyyar a jihar.

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

A wani labarin, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi gargadin cewa idan har manyan APC basu dauki cikakkiyar iko kan jam’iyyar ba a jihar Kano, toh za su iya shank aye a zaben 2023, jaridar Guardian ta rahoto.

Doguwa na so Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbi ragamar kula da harkokin jam’iyyar mai mulki don duba yadda tsohon kwamishinan harkokin kananan hukumomi kuma dan takarar mataimakin gwamnan APC, Murtala Garo ke wuce gona da iri.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano kan sabon rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar, Doguwa ya koka cewa idan har ba a magance batun ficewar mamabobin majalisar dokokin kasa bakwai ba a Kano, APC na iya rasa mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel