An Samu Gawar Matar da ta Kama Daki Tare da Namiji a Legas

An Samu Gawar Matar da ta Kama Daki Tare da Namiji a Legas

  • Manajan wani otal a Igbogbo dake Ikorodu a Legas ya tsinta gawar wata mata mai suna Muinat a dakin da suka kama da wani Alfa Sule
  • Kamar yadda aka gano, Alfa Sule da matar sun isa otal din tare da kama daki a ranar Juma’a, amma Alfa Sule yayi batan dabo sai gawar matar aka gani
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, yace Bajaj din Alfa Sule yana nan kuma an fara nemansa tare da binciken abinda ya kashe matar

Legas - Manajan wani otal dake Igbogbo dake yankin Ikorodu a jihar a Legas ya tsinta gawar wata mata a daya daga cikin dakunan otal din a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Taswirar Legas
An Samu Gawar Matar da ta Kama Daki Tare da Namiji a Legas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan yayin da ya zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Amurka.

Kara karanta wannan

Lokaci Yayi: Kyawawan Hotunan Kafin aure na Jaruma Halima Atete da Angonta

Hundeyin yace manajan otal din ya kai korafin ofishin ‘yan sanda dake Ikorodu, jaridar The Nation ta rahoto.

Yace rahoton manajan ya bayyana cewa, matar mai shekaru 46 a duniya ta isa otal din a babur kirar Bajaj wacce wani Alfa Sule ya tuko a ranar Juma’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace manajan ya bada rahoton cewa, Alfa Sule wanda ba a san daga inda yake ba, sun kama dakin tare da matar wacce daga bisani aka gano sunanta da Muinat.

An ga gawa amma namijin da suke tare yayi batan dabo

Hundeyin yace yayin da manajan ke zagaya dakunan a ranar Asabar wurin karfe 6 na safe, ya ga gawar matar amma Alfa Sule yayi batan dabo.

“Babu wata alama ta fada a jikin matar, Alfa Sule kuwa yayi batan dabo amma ya bar babur dinsa.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Burma Wa Saurayinta Sadiq Ɗahiru Wuka Har Lahira

“‘Yan Sanda sun ziyarci wurin kuma sun samu gawar tana fitar da kumfa daga hancinta. An dauka hotunan wurin kafin a mika gawar zuwa ma’adanar gawawwaki dake babban asibitin Ikorodu don duba abinda ya kashe ta.”

- Yace.

Manajan otal na taimakawa wurin bincike

Hundeyin ya kara da cewa manajan otal din yana taimakawa ‘yan sanda wurin bincike yayin da ake ta kokarin damko Alfa Sule da ya tsere.

Yace za a mika lamarin zuwa sashen binciken kisan kai na ‘yan sanda dake Panti a Yaba domin cigaba da bincike.

An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota

A wani labari na daban, an tsinta gawar wani magidanci da wata budurwa a yankin Isolo dake jihar Legas.

An gano cewa, motar kirar SUV ta dade a tsaye tun daren jiya a wurin inda daga bisani ‘yan anguwar suka ankare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng