Jam’iyyar APC Ta Rasa ‘Ya’yanta 1,000, Sun Fice Zuwa PDP a Jihar Lagas

Jam’iyyar APC Ta Rasa ‘Ya’yanta 1,000, Sun Fice Zuwa PDP a Jihar Lagas

  • Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi babban kamu a jihar Lagas gabannin babban zaben 2023 mai zuwa
  • Mambobin APC kimanin su 1,000 sun fice daga jam’iyyar mai mulki zuwa cikin su Atiku Abubakar
  • Masu sauya shekar sun bayyana rashin damokradiyya a cikin jam’iyyar APC a matsayin dalilinsu na karawa gaba

Lagos - Kimanin mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 1,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Lagos Mainland da ke jihar Lagas.

Masu sauya shekar wadanda suka samu jagorancin Nurudeen Dauda sun bayyana rashin damokradiyya a jam’iyyar mai mulki daga cikin dalilansu na barin jam’iyyar, jaridar Leadership ta rahoto.

APC da PDP
Jam’iyyar APC Ta Rasa ‘Ya’yanta 1,000, Sun Fice Zuwa PDP a Jihar Lagas Hoto: PM News
Asali: UGC

Akwai karin yan APC da zasu dawo PDP nan gaba kadan, jagoran masu sauya shekar

Masu sauya shekar wadanda suka fito daga Ward J, yankin Iwaya na karamar hukumar, sun samu tarba daga by Dr. Adetokunboh Pearse da shugaban PDP a karamar hukumar, Mista Malomo Adelabi.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Gamu da Cikas, Hadiman Gwamnan Arewa Sun Fice Daga PDP Zuwa Wata Jam'iyya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daudu, wanda ya kasance hadimin Hon. Olanrewaju Oshun, mamba mai wakiltan Lagos Mainland II a majalisar dokokin jihar, ya ce akwai karin ‘yan APC da zasu dawo PDP kwanan nan.

Yayin da yake godiya ga shugabannin jam’iyyar adawa a jihar kan karbarsu da suka yi, ya yi zargin cewa an binne muradai da takara da dama a APC saboda rashin damokradiyyar cikin gida.

PDP zata baku damar cimma muradanku, Dr Pearse ga masu sauya sheka

Yayin da yake yiwa masu sauya shekar maraba a jihar, Dr Pearse wanda mamba ne a kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa, kuma darakta a matakin farko ya basu tabbacin samun adalci da damawa dasu a PDP sannan za a basu damar cimma muradansu.

Dr Pearse, wanda ya yiwa masu sauya shekar addu’an cimma muradansu, ya bayyana cewa PDP ce jam’iyya mafi yanci da tasiri a kasar nan, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu da Sanata Adamu Sun Gana da Shugaba Buhari Bayan Dawowarsa Najeriya daga Landan

Ya ce:

“Barkanku da zuwa. Da shigowarku mun tabbatar da cewar PDP zata kwace jihar Lagas.”

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan har yayi nasarar zama shugaban kasa, gwamnatinsa zata hada kan yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel