Hawaye Sun Kwaranya: An yi Jana'izar Dan Majalisan APC Da Ya Mutu Wajen Kamfe

Hawaye Sun Kwaranya: An yi Jana'izar Dan Majalisan APC Da Ya Mutu Wajen Kamfe

  • An yi jana'izar dan majalisar dokokin jihar Legas wanda ya yane jiki ya fadi bayan kamfen jam'iyyar APC a Jos ranar Talata
  • A ranar Laraba an mayar da gawarsa jihar Legas daga Jos kuma an bizne shi bisa koyarwan Musulunci
  • Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai Gwamnan Legas, mataimakinsa, da sauran yan majalisa

Hawaye sun kwaranya ranar Laraba yayinda aka yi jana'izar dan majalisar dokokin jihar Legas, Hon. Abdul-Sobur Olayiwola Olawale, wanda ya rasu ranar Talata, 15 ga Nuwamba a Jos, jihar Plateau.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Mudashiru Obasa, ya jagoranci daukacin yan majalisa da ma'aikatan majalisar wajen jana'izar.

Gawar mamacin ta dira tashar jirgin Murtala dake Legas ne da rana da aka kaita gidansa a Legas.

Janaiza
Hawaye Sun Kwaranya Yayinda Akayi Jana'izar Dan Majalisan APC Da Ya Mutu Wajen Kamfe Hoto: Eromosele Ebhomele
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Soji sun Halaka Kachalla Gudau, Kwamandan ‘Yan Bindiga da Ya Shahara a Satar Shanu da Dillancin Kwayoyi

Daga baya aka kai ta Ebony Vaults inda Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, da mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat, suka halarta.

Sakataren Yada labaran Kakakin majalisar Legas, Eromosele Ebhomele, ya bayyana hakan a sakon da ya aikewa Legit.ng.

Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai matarsa, 'yayansa, makwabta, da abokan arziki.

Wata majiya ta bayyana cewa yanzu haka ana saura kwanaki 16 da auren daya daga cikin 'yayansa mata sukayi wannan babban rashi.

Kalli hotunan jana'izar

Jana'iza
Hawaye Sun Kwaranya Yayinda Akayi Jana'izar Dan Majalisan APC Da Ya Mutu Wajen Kamfe Hoto: Eromosele Ebhomele
Asali: Facebook

Yadda ‘Dan Majalisar Legas Ya Rasu Wajen Taron Kamfe

Sabbin bayanai sun fito game da mutuwar marigayi.

Jaridar Vanguard ta zanna da wani wanda abin ya faru a gaban idonsa amma ya bukaci a sakaye sunansa.

A cewar majiyar, dandazon mutane suka dura kan Honarabul Olawale a filin wasan da aka bude takarar Bola Tinubu/Kashim Shettima.

“Olawale bai yi sa’a ba, yana kokarin neman hanya a cikin dandazon jama’a, sai suka danne shi a wajen taron bude yakin neman zaben APC.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Yi Magana Kan Ɗan Majalisar da Ya Rasu a Wurin Gangamin Yakin Neman Zabensa

Amma mun rungumi kaddarar Ubangiji."

- a cewar Majiya

Kafin rasuwarsa, Hanarabul Abdu Sobur Olawale ya kasance shugaban kwamitin harkokin kananan hukumomi da alaka da al’umma na majalisa, ‘dan siyasar yana kan wa’adinsa na biyu a majalisa.

Kafin wannan lamarin ya auku, Omititi yana gagarumin shirye-shiryen auren da diyarsa. An sa rana za ayi auren ne nan da makonni biyu a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel