Labaran Duniya
Lucile Randon, wacce aka fi sani da Siater Andre ita ce mutum da tafi kowanne 'dan Adam tsufa a duniya ta rasu tana da shekaru 118 a duniya a birnin Toulon.
Wani Malamin Majami'a a kasar Brazil, Felisberto Sampaio, tare da matarsa sun gamu da ajalinsu yayin da suka shiga Teku domin ceto dansu dake gab da nutsewa.
Rahotanni daga Nepal sun nuna cewa akalla mutane 16 suka rasa rayuwarsu lokacin jirgin sama makare da fasinjoji 72 ya yi hadari ranar Lahadi, ana kokarin ceto.
Bidiyon wata karamar yarinya da ta tashi cikin karnuka biyar ya ba jama'a mamaki. Ta koma rayuwa kamar karnukan inda ta ke tafiya kamar su da kafa da hannu.
Wata budurwa ta kama gidan haya ita kadai sai dai babu kayan daki illa gado kawai a gidan, a bidiyon da ta wallafa ta ce iya abin da kudin ta kawai zai iya siya
A wani bidiyo da aka wallafa a Instagram, wata tsohuwa ta bayyana yadda aka yi garkuwa da ita kuma aka bar ta cikin birai.Da su ta saba kuma take samun natsuwa.
Hukumomi a kasar Australia sun tabbatar da faruwar hatsari tsakanin jiragen Helikwafta biyu ranar Litinin, akalla mutum hudu sun kwanta dama wasu na Asibiti.
Shahararren hamshakin mai arzikin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $200 biliyan a cikin shekarar 2022 kuma ya kafa tarihin nan a duniya. Ya rasa matsayinsa.
Jirgin Helikwafta na rundunar sojojin kasar Nijar ya yi hatsari yana shirin sauka a sansani, ma'aikatar tsaro tace baki ɗaya mutane uku dake ciki sun mutu.
Labaran Duniya
Samu kari