Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Hari kusa da Masallacin Juma'a na Jami'ar Usman Danfodio
- ’Yan bindiga sun kai hari a Gidan Asarki da ke bayan Babban Masallacin Juma’a na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato
- Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun harbi wani mai shanu a ƙafa tare da sace shanu 28
- Rundunar ’yan sandan Sakkwato ta tabbatar da kai harin, amma babu rahoton mutuwa ko sace mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Wasu ’yan bindiga sun kai hari a Gidan Asarki, wata al’umma da ke bayan Masallacin Juma’a na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato (UDUS) da ke jihar Sakkwato.
An ruwaito cewa maharan sun harbi wani mai shanu a ƙafa tare da sace shanu 28 yayin wannan hari da ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na dare ranar Lahadi.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ruwaito vewa lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba bayan da maharan suka buɗe wuta jim kaɗan da isowarsu yankin jami’ar.
Yan bindiga sun nemi dalibai
Mazauna yankin sun ce maharan sun yi musu barazana tare da neman a fito da ɗaliban da ke zaune a yankin. Sai dai harin ya faru ne a lokacin hutun jami’a, inda aka ce ɗalibai da dama sun tafi gida.
“Sun yi mana barazanar cewa mu fito da ɗaliban da ke zaune a cikinmu, amma muna godiya ga Allah da abin ya faru a lokacin hutu,” in ji wani mazaunin yankin.
Daga bisani, maharan sun karkata hankalinsu zuwa ga dabbobi, inda suka kwashe shanun mazauna yankin. An ce sun harbi wani mai shanu a ƙafa ne bayan ya yi ƙoƙarin hana su kwashe dabbobinsa.
Hussaini, wani mazaunin yankin da ya ziyarci al’ummar a safiyar Litinin, ya ce wanda aka harba ya tsira, kuma an kai shi asibiti domin yi masa magani.
“Yayin da suke harbi, sun harbi wani dattijo a ƙafa, amma yana da rai, kuma mun kai shi asibiti,” in ji shi.
Mahara sun sace shanu a Sakkwato
Sai dai rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da cewa an sace shanu 28 a yayin harin.
Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Rufai, ya ce maharan sun kai hari a yankin tare da harbin mutum guda a ƙafa.
“Sun kai hari a ƙauyen Gidan Asarki, suka harbi mutum guda a ƙafa tare da sace shanu 28,” in ji Rufai.
Kakakin yan sandan ya bayyana cewa wurin ƙauye ne da ke bayan Masallacin Juma’a na jami’ar.

Source: Twitter
Lamarin ya sake tayar da hankula kan tsaron al’ummomin da ke kewaye da jami’ar UDUS, musamman ƙauyukan da ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga da satar dabbobi.
Yan bindiga sun kase malamin makaranta
Kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani sabon malamin makaranta a Jihar Sokoto , Maniru Sa’adu Imam.
' Yan bindigan sun kashe shi ne sa’o’i kaɗan bayan ya halarci aikin tantance bayanan ma’aikata domin fara karɓar albashi a cikin birnin Sokoto.
Asali: Legit.ng

