Zaben 2027: Kashim Shettima Ya Dura kan Peter Obi, Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo

Zaben 2027: Kashim Shettima Ya Dura kan Peter Obi, Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo

  • Kashim Shettima ya ce Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, ba shi da abin da zai gabatar wa ’yan Najeriya fiye da ambaton alkaluma
  • Shettima ya kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa farashin litar mai a wasu kasashen Afirka makwabta ya fi na Najeriya tsada
  • Mataimakin shugaban kasar ya bukaci masana tattalin arziki su goyi bayan manufofin gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi.

Kashim Shettima ya bayyana cewa babu wani abu na musamman da zai iya gabatar wa ’yan Najeriya baya ga ambaton alkaluman tattalin arziki.

Shettima ya caccaki Peter Obi
Peter Obi da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Hoto: Hon. Saifullahi Hassan, Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Shettima ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin Najeriya su goyi bayan manufofin gwamnatin tarayya, cewar rahoton ThePunch.

Kara karanta wannan

APC ta koma ba Atiku shawara kan abin da ya kamata ya yi wa Tinubu a zaben 2027

Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauka.

Me Shettima ya ce kan Peter Obi?

Mataimakin shugaban kasar ya ce yana girmama Obi saboda ya fito fili ya bayyana cewa ba zai dawo da tallafin man fetur ba idan ya zama shugaban kasa.

Sai dai ya ce hakan bai wadatar wajen nuna abin da tsohon gwamnan Anambra zai iya yi wa kasar ba.

“Ina girmama Peter Obi saboda jajircewarsa na cewa ba zai dawo da tallafin man fetur ba, amma bayan yawan ambaton wasu alkaluma, Mista Peter Obi ba shi da wani abu da zai gabatar wa ’yan Najeriya.” In ji shi.

Ya kara da cewa Obi ya dogara ne da alkaluman tattalin arziki, sannan ya yi kira ga fitattun masana tattalin arzikin kasar da su mara wa gwamnatin tarayya baya.

Shettima ya magantu kan farashin man fetur

Kara karanta wannan

Ana zargin Tinubu na cikin wani hali, bai san ma waye shugaban ƙasa ba

A yayin kare matakin cire tallafin man fetur, Shettima ya kwatanta farashin litar mai a Najeriya da na wasu kasashen da ke makwabtaka da ita.

Ya ce a wasu shekarun baya, Najeriya tana amfani da kusan lita miliyan 67 na man fetur a kowace rana, lamarin da ya nuna girman amfani da man a kasar a lokacin.

A cewarsa, farashin litar man fetur a Jamhuriyar Nijar ya kai kusan Naira 1,148.36, yayin da a Jamhuriyar Benin yake Naira 1,729.29, sannan a Kamaru ya kai naira 1,945.50.

Shettima ya ce a Najeriya kuwa, farashin litar man ya kai naira 1,390. Ya bayyana cewa bambancin farashin ya nuna irin tasirin tsarin farashin man fetur da Najeriya ta yi amfani da shi a baya.

Mataimakin shugaban kasar ya ce:

“Bambancin yana da yawa. Najeriya ta kasance kamar bikin Kirsimeti ga sauran kasashen Afirka.”

Muhawara kan cire tallafin man fetur

Kalaman Shettima na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan cire tallafin man fetur da kuma tasirinsa ga tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin Tinubu ta kare matakin a matsayin wani bangare na manufofinta na tattalin arziki, yayin da Peter Obi da sauran ’yan adawa ke sukar wasu bangarorin yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Sheikh Pakistan ya faɗi aikin Tinubu a Kano da ya cancanci a zaɓe shi a 2027

Shettima ya soki Peter Obi
Kashim Shettima a wajen taron APC a Kaduna Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Shettima ya nemi alfaramar 'yan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya mika bukatarsa ga masu zabe a yankin Arewacin Najeriya.

Shettima ya buƙaci masu zaɓe a yankin Arewa su haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng