Sarauniyar Kyau: Hotunan Sarauniyar Kyau Ta Thailand Sanye Da Tufafi Da Ake Kera Da Mabudin Lemun Gwangwani

Sarauniyar Kyau: Hotunan Sarauniyar Kyau Ta Thailand Sanye Da Tufafi Da Ake Kera Da Mabudin Lemun Gwangwani

  • Yayin gasar sarauniyar kyau na Thailand, Anna Sueangam-iam, sarauniyar kyau ta Thailand, ta saka tufafi da aka yi da mabudin lemun gwangwani
  • A cewar rahotanni, ta saka tufafin ne saboda iyayenta - mahaifinta dan gwangwan ne kuma mahaifiyarta mai sharar titi ne a Bangkok
  • Wani kamfani mai yin tufafi a kasar Thailand ne ya tsara tufafin da aka nada wa suna 'Hidden Precious Diamond'

Thailand - Duk da cewa an kammala gasar sarauniyar kyau na duniya na shekarar 2023, akwai wasu abubuwa daga taron da suka kayatar da mutane.

Anna Sueangam-iam, sarauniyar kyau ta Thailand, ta fito fili sanya da tufafi na fita da dare wanda ya dace da surar jikinta.

Miss Thailand
Sarauniyar Kyau: Hotunan Sarauniyar Kyau Ta Thailand Sanye Da Tufafi Da Ake Kera Da Mabudin Lemun Gwangwani. Hoto: Credit: @annasnga_1o, @thekimrlln
Asali: Instagram

Idan an masa kallon farko, tufafin ya yi kama da irin tufafin mata da aka saba gani amma idan an kura ido sosai za a gane daban ya ke.

Kara karanta wannan

“Kina Karawa Addinin Musulunci Kyau”: Jaruma Mercy Aigbe Ta Nunawa Duniya Mijinta Yayin da Suke Aikin Hajji

An kere tufafin ne da mabudin lemun gwangwani. Sarauniyar kyau din ta zabi tufafin ne domin ta karrama iyayenta - mahaifinta dan gwangwan ne kuma mahaifiyarta mai sharar titi ne a Bangkok.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani kamfani da ke kasar Thailand ne ya kera tufafin da aka saka wa suna 'Hidden Precious Diamond Dress'

My Modern Met ya rahoto cewa an yi tufafin ne da mabudin lemun gwangwani na aluminium da Swarovski crystals.

An wallafa hotunan Anna a shafinta da wannan rubutun:

"Yanayin wurin da na girma ya bani tunanin yin wannan tufafin. Na tashi da mahaifi mai sana'ar gwangwan. An yi wannan tufafin ne da gwangwan da aka zubar da wasu kayan, mai suna 'Can Tab' don nuna wa duniya cewa abin da ake dauka bai da amfani yana da kimarsa da kyau."

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'adda Sun Kashe Basarake Bisa Kuskure, Sun Sace Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Ga abin da aka wallafa a kasa:

Tsaleliyar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasar Poland Don Bikin Kirsimeti

Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna wata budurwa farar fata da sauryinta dan Najeriya a kasar Poland lokacin kirsimeti.

Matar ta ce ta gayyaci saurayin ne domin ya samu damar ganawa da danginta da sauran yan gidansu.

Kamar yadda aka gani a faifan bidiyon, budurwar ta dafa abinci sannan saurayin da yan uwanta suna zaune a teburi tana saka musu abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel