Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

  • Wata mata ‘yar ƙasar Ecuador, Bella Montoya, ta farka a cikin akwatin gawarta a lokacin da ake shirin kai ta makwanci
  • A ranar 9 ga watan Yuni ne aka ayyana bisa kuskure cewa Montoya ta rasu, wacce ana ƙoƙarin kai ta makwanci ne ta farfaɗo
  • An ajiye Montoya a asibiti bayan faruwar lamarin, sai dai kuma abin takaici, ta mutu sakamakon bugun jini a ranar Juma'ar da ta gabata

Bidiyon wata tsohuwa ‘yar ƙasar Ecuador da ta farfaɗo bayan sanyata cikin akwatin gawa ya karaɗe kafen sada zumunta a makon da ya gabata.

Sai dai hukumomi a ranar Lahadi, sun sanar da cewa, matar ta mutu daga baya, kamar yadda The Punch ta wallafa.

Wata mata ta farko daga cikin akwatin gawa
Wata mata da ta farko a akwatin gawata ta sheƙa a karo na biyu. Hoto: NBC News
Asali: UGC

A cikin wani dan gajeren bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a makon da ya gabata, an ga matar mai suna Bella Montoya, 'yar shekara 76, a cikin buɗaɗɗen akwatin gawarta tana numfashi sosai yayin da wasu maza biyu ke ƙoƙarin taimaka ma ta.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode

An sanar da rasuwar matar bisa kuskure

Ɗan ta, Gilbert Barbera, ya ce ta ɗauki lokaci mai tsawo tana dukan akwatin daga ciki, a ƙoƙarin ganin ta fito, a yayin da 'yan uwanta ke jimamin rasuwar ta ta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An sanar da cewa ta mutu ne a ranar 9 ga watan Yuni a bisa kuskure.

Bayan irin wahalhalu da fargabar da ta fuskanta bayan farkowarta, an ajiye Montoya a wani asibiti da ke garin Babahoyo.

Ma’aikatar lafiya ta yankin da lamarin ya faru, ta tabbatar da cewa, matar ta rasu daga baya, sakamakon bugun jini a ranar Juma’a.

NBC News ta ruwaito Barbera ya na fadar cewa mahaifiyar tasa ta rasu da gaske a wannan karon.

Hukumomin lafiya sun sa a gudanar da bincike

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ba da umarnin gudanar da bincike kan yadda aka ayyana cewa matar ta mutu bisa kuskure a karon farko.

Kara karanta wannan

Amarya Ta Kai Ango Ƙara Kotu, Ta Nemi a Raba Auren Saboda Yana da Matsalar Ruwan Kwayar Halitta

Rahotannin dai na nuni da cewa Montoya ta sha fama da wata iriyar cuta mai suna catalepsy, wacce ke sanya mutum fita hayyacinsa sannan kuma jikinsa ya sandare.

Ɗan nata ya shaidawa manema labarai cewa za a binne ta a wata makabartar al'umma, sannan kuma an dawo da gawarta zuwa gidan jana'izar da ta tashi.

'Yar shekara 70 da ba ta taɓa aure ba ta bayyana kalar mijin da take so

A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa wata mata mai kimanin shekaru 70 da ba ta taɓa yin aure a duniya ba ta bayyana irin namijin da take so ta aura.

Matar mai suna Genevieve, ta bayyana cewa saurayi ɗan kimanin shekaru 21 take da burin ta aura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel