Farfesa Makari Ya Yi Magana kan Kashe Sheikh Masussuka

Farfesa Makari Ya Yi Magana kan Kashe Sheikh Masussuka

  • Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya yi Allah wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka a jihar Katsina
  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya bayyana kisan malamin a matsayin zalunci ga marigayin, iyalansa da ɗalibansa
  • Sun yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, tare da kira a kare rayukan mutanen da ke bayyana abin da suka yi imani da shi ba tare da fargaba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, da tsohon hadimin shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, sun yi Allah wadai da kisan malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a jihar Katsina.

Farfesa Makari ya bayyana damuwarsa kan kisan, yana mai cewa abin da ya faru na iya zama makomar duk wanda yake son bayyana abin da ya yi imani da shi, amma ra’ayinsa ya saɓa da na masu amfani da makamai.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya fadi matakin da za a dauka kan kashe Masussuka

Sheikh Ibrahim Makari da Yahaya Masussuka
Sheikh Ibrahim Makari da Yahaya Masussuka. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari|Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

Abin da Farfesa Makari ya ce

Farfesa Makari ya bayyana ra’ayinsa ne a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, inda ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan Sheikh Masussuka, Ya kuma gafarta masa kurakuransa.

Ya ce:

“Ƙarshen Sheikh Masussuka ita ce makomar duk wanda ya shirya faɗin abin da ya yi imani da shi, wanda ya saɓa da abin da masu makamai a hannu suke son a faɗa.”

Limamin ya ƙara da cewa:

“Kada Allah Ya kawo ranar da duk mai son faɗin abin da ya yi imani da shi sai ya tanadi makami domin kare kansa daga waɗanda suke da saɓanin fahimta da shi.”

Bayanin Bashir Ahmad

A nasa martanin, Bashir Ahmad ya bayyana cewa ya samu labarin kisan Sheikh Masussuka cikin alhini, yana mai cewa an kashe malamin ne a gidansa a gaban iyalansa.

A sakon da ya wallafa a Facebook, ya ce kashe mutum a gidansa tare da jefa iyalansa cikin irin wannan mummunan yanayi babban zalunci ne.

Kara karanta wannan

Sudais ya magantu da bama baman Houthi suka kusa isa Makkah da Madina

Bashir Ahmad ya bayyana cewa ko da yake bai taɓa shiga batun koyarwa ko akidar Sheikh Masussuka ba, hakan ba zai hana shi yin Allah wadai da kisan ba.

Sheikh Yahaya Masussuka
Sheikh Masussuka da aka kashe a Katsina. Hoto: Sheikh Yahya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

Ya ce bambancin aqida ko rashin amincewa da koyarwar mutum ba ya ba kowa damar kashe shi ko tauye masa haƙƙin rayuwa.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Masussuka bayan wani hari da aka kai masa da yammacin ranar Litinin, 26 ga Oktoban 2026.

Bayanin gwamnan Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi jimamin kisan Sheikh Yahaya Masussuka.

Gwamnan ya ce jami’an tsaro za su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka kashe malamin da wani abokinsa a wajen gidansa da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma.

Radda ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu, su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da guje wa duk wani mataki da ka iya haddasa tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng