Matashi Mara Hannuwa Ya Zama Tela, Ya Ɗinka Kaya a Cikin Wani Bidiyo

Matashi Mara Hannuwa Ya Zama Tela, Ya Ɗinka Kaya a Cikin Wani Bidiyo

  • Wani matashi musaki mara hannuwa ya ƙi yarda zuciyar sa ta mutu, inda yaje ya koyi sana'ar ɗinki
  • A wani bidiyo da ya yaɗu a TikTok, yana nuna yadda matashin yake sarrafa keken ɗinki cikin ƙwarewa
  • Bidiyon ya nuna cewa matashin baya da hannuwa inda suka yi kama da gundulmi alamar kamar an yanke su

Wani matashi mara hannuwa yasha yabo sosai a TikTok saboda yadda ya dage ya zama ƙwararren tela, domin cin gashin kansa.

A wani bidiyo da @saubekandeumw ya sanya, ya nuna matashin yana da gundulmin hannu domin hannuwan sa sun yi kama da an yanke su daga wuyan hannu.

Matashi
Matashi Mara Hannuwa Ya Zama Tela, Ya Ɗinka Kaya a Cikin Wani Bidiyo Hoto: TikTok/@saubekandeumw
Asali: UGC

Jajircewar sa wajen ganin ya nemi na kan sa duk da halin da yake ciki ya sanya yasha yabo sosai a wajen masu amfani da TikTok.

Wani abu da ya ɗauki hankali a cikin bidiyon shine lokacin da matashin yayk amfani da gundulmin hannun sa ya sanya tsare a cikin allurar ɗinkin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da rashin hannun sa ya sanya zare cikin allura

Duk da ƙanƙantar da allura take da ita, sai da matashin ya sanya zare a cikin ta ba tare da amfani da hannuwan sa ba.

Bayan ya samu nasarar yin hakan, sai ya fara ɗinka kayan inda yake amfani da hannun sa wajen daidaita kayan a saman keken dinkin.

Ƙwarewar sa wajen ɗinkin da kuma jajircewar da yake da ita na ganin ya tashi yayi ya samu na kanshi, ya burge mutane sosai a TikTok.

Ga kaɗan daga cikin abinda mutane ke cewa:

@adama ta rubuta:

"Allah yayi maka albarka.

@user7980821616629 ya rubuta:

"Allah zai albarkaci aikin da kake yi ɗan'uwa."

@Maame Esi ta rubuta:

"Allah yayi maka albarka ɗan'uwa."

Abin Mamaki: Bidiyon Yadda Wata Budurwa Ke Sarrafa Ƙafafun Ta Ya Ɗauki Hankula Sosai

A wani labarin na daban kuma wata budurwa ta ɗauki hankula sosai a yanar gizo bisa yadda take sarrafa ƙafafun ta.

Buddurwar.dai bata da hannuwa amma hakan bai hanata sarrafa ƙafafun ta wajen yin wasu abubuwa na masu hannuwa cikin ƙwarewa ba.

Budurwar dai ta yi amfani ƙafafun ta wajen sarrafa su cikin wani yanayi na ƙwarewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel