Wannan Akwai Ja'ira: Daliba Ta Tayar Da Gobara a Makaranta Kan An Kwace Mata Waya

Wannan Akwai Ja'ira: Daliba Ta Tayar Da Gobara a Makaranta Kan An Kwace Mata Waya

  • Wata ɗaliba ƴar makaranta ta biyewa fushin zuciya inda ta salwantar da rayukan sauran ƴan'uwan ta ɗalibai mata
  • Ɗalibar dai ta tayar da gobara ne a ɗakin ƙwanansu na ɗalibai wacce ta yi sanadiyyar halaka mutane 19
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ɗalibar wacce ita ma ta ƙone a gobarar, ta yi wannan katoɓarar ne don an kwace mata waya

Guyana - Hukumomi a Guyana sun bayyana cewa wata ɗaliba da aka kwace wa waya a makaranta, ta fusata inda ta tayar da gagarumar gobara a ɗakin kwanan ƴan uwanta ɗalibai a wata makaranta.

Gobarar wacce ta tashi a ƙasar ta Latin Amurka a daren ranar Litinin, ta janyo asarar rayukan mutum 19, waɗanda da yawa daga cikinsu ɗalibai ne mata, rahoton BBC Hausa ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

Daliba ta tayar da gobara a makaranta
Budurwar ta fusata ne saboda an yi mata hukunci Hoto: Bbchausa.com
Asali: UGC

Ɗaliban sun kasa samun damar tserewa ne saboda an rufe ɗakin, sannan tagoginsa a kulle su ke.

Ɗalibar wacce ta aikata wannan ta'asar dai ƴar shekara goma sha ce, kuma har da ita gobarar ta ritsa, inda yanzu haka tana kwance a asibiti, sannan rahotanni sun tabbatar da ta amsa cewa ita ta tayar da gobarar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sheda ya bayyana cewa hukumomi na ta tunanin abin yi na shin ko za su tuhume ta da laifin tayar da wutar.

Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne daga wurin ban-ɗaki sannan ta kama ginin gaba ɗaya wanda na katako ne da ke dauke da ɗalibai 57 a lokacin.

Waɗanda suka tsallake rijiya da baya a gobarar a garin Mahdia na tsakiyar ƙasar sun ce ihu da kururuwar da suka ji a cikin dare ne suka tashe su.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Sanatan NNPP a Jihar Nasarawa, Ya Sha Da Kyar a Wani Mummunan Hari Da Aka Kai Masa

Ɗalibar ta fusata bayan an hukunta ta

Bayanai sun nuna cewa yarinyar ta yi barazanar aikata abin bayan da aka hukunta ta saboda tana alaƙa da wani namiji babba wanda ya girme ta.

Yan kwana-kwana sun rika fasa tagogin ginin ne kafin su iya ceto mutanen da suka tsira da ransu.

Wasu ɗaliban sun ƙone sosai ta yadda sai an yi gwajin ƙwayoyin halitta kafin a iya gane gawarwakin.

Shugaban ƙasar Irfaan Ali da farko ya bayyana lamarin a matsayin babban bala'i.

Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Agbeni Da Ke Jihar Oyo

A wani labarin na daban kuma, wata mummunar gobara ta tashi a wata fitacciyar kasuwa da ke a jihar Oyo.

Gobarar ta tashi ne a kasuwar Agbeni da ke a cikin birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda ta janyo asarar miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel