Bakaniken Da Ya Mayar Da Miliyan 10 Ya Bayyana Kudin Da Aka Bashi Matsayin Tukwici

Bakaniken Da Ya Mayar Da Miliyan 10 Ya Bayyana Kudin Da Aka Bashi Matsayin Tukwici

  • Bakaniken nan ɗan Najeriya wanda labarin sa ya yaɗu bayan ya dawo da N10.8m da aka tura masa a asusun bankin sa yace baya da lafiya
  • Timothy yace ciwon kai ya kama shi sannan ya bayyana yawan kuɗin da aka ba shi bayan yayi wannan namijin ƙoƙarin
  • Mutane da dama sun yi ta cece-kuce kan ladan dawo da kuɗin sa aka ba shi, wasu na cewa sun yi kaɗan, wasu kuma sun ce ba haka ba

Bayan ya mayar da N10.8m da aka tura masa cikin asusun ajiyar sa na banki bisa kuskure, bakaniken nan Timothy, ya ce an ba shi ladan naira dubu hamsin.

Ɗaya daga cikin kwastomomin sa mai suna Chinonso Ndukwe, shine ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook, inda yace ya ji hakan ne daga bakin Timothy bayan ya haɗu da shi ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Gida Najeriya Zan Dawo": Kyakkyawar Budurwa Mai Rayuwa a Kasar Waje Ta Koka Kan Rashin Samun Saurayi, Bidiyonta Ya Yadu

Bakanike
Bakaniken Da Ya Mayar Da N10.8m Ya Bayyana Kudin Da Aka Bashi Matsayin Tukuici Hoto: Facebook/Chinonso Ndukwe, Twitter/Henshawkate
Asali: Facebook

Yayin da ya sanya hoton su tare da Timothy, Chinonso yace bakaniken ya daɗe yana masa aiki mai kyau kuma ya yaba da halin ƙwaran da ya nuna bayan ya ga labarin a yanar gizo.

Ya ƙara da cewa Timothy baya da lafiya lokacin da suka haɗu inda bakaniken ya gaya masa cewa ciwon kai ne ke damun sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Chinonso ya nuna rashin jindaɗin sa kan cewa ɗan kwangilar da aka mayarwa kuɗin naira dubu hamsin kawai ya ba Timothy.

A kalamansa:

"Kafin na wuce zuwa TV na je wajen bakanike na domin na tambaye shi game da labarin da na gani ya yaɗu a intanet jiya."
"Yana yi min aiki mai kyau. Lokacin da na ji cewa ya mayar da N10.8m ga ɗaya daga cikin kwastomomin sa, na yaɓa sosai."
"Yau lokacin da na haɗu da shi baya da lafiya. Yace min ciwon kai ke damun sa. Mutumin da ya mayarwa da kuɗin sa N50,000.00 ya ba shi. Mutane na da abin mamaki. Lallai!"

Kara karanta wannan

Likita Ya Faɗa Wa Wani Mutumi Kar Ya Kusanci Matarsa Saboda Abu 1, Da Suka Koma Gida Ya Ba Da Mamaki a Bidiyo

Mutane sun yi ta cece-kuce

Andrew Ezeudegbe ya rubuta:

"Yayi abinda yakamata ace yayi. Kudin ba na shi bane. Idan ya cinye su, tabbas sai ya biya ninkin hakan. Saboda haka a kula.

Chimeson Ifē Adigo said:

"Nawa o. Wannan koyarwar ta ku cewa duk wani abin kirki sai an bayar da tukuici a kan sa ya fara taɓa yadda kuke kallon abubuwa a rayuwa."

Kris Brown ya rubuta:

"Biko 50k tayi kaɗan da yawa, mu gayawa kan mu gaskiya. Mutum ya dawo N10.8m ba tare da wata jarfa ba amma wasu na nan nata rubuta shirme. Odan da ace ya cinye kuɗin fa? Mtcheeeew."

Wani Bidiyon Dattijo Da Aka Yiwa Kyautar Kudi Ya Fashe Da Kuka Ya Sosa Zuciya

A wani labarin na daban kuma, bidiyon wani tsoho da aka yiwa kyautar kudi ya sanya zubar da ƙwalla.

Dattijon dai ya fashe da kuka bayan an miƙa masa kyautar kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel