Trump Ya Fara Ganin Ta Kan Shi, Mutuminsa Ya Sha Kasa a Zaben Brazil
- Shugaban kasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya sake lashe zaben shugaban kasa, inda ya samu nasarar doke Sanata Flávio Bolsonaro, wanda ke da alaƙa da Donald Trump
- Lula mai shekaru 80 ya samu sama da kashi 51 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Bolsonaro ya ƙi amincewa da sakamakon zaben tare da cewa zai tafi kotu
- Nasarar Lula ta zo ne bayan yakin neman zabe da ya fi mayar da hankali kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da kuma cin hanci da rashawa a fadi kasar Brazil
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Brazil – Shugaban kasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya sake lashe zaben shugaban kasa, inda ya doke abokin hamayyarsa, Sanata Flávio Bolsonaro, domin samun wa'adi na huɗu a tarihi.
Lula mai shekaru 80 ya samu sama da kashi 51 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a zagaye na biyu na zaben.

Source: Getty Images
CNN ta wallafa cewa Bolsonaro, wanda ke da alaƙa da Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce ba zai amince da sakamakon zaben ba, inda ya bayyana aniyarsa ta shigar da ƙara domin neman soke shi.
Bolsonaro ya ƙi amincewa
Bolsonaro, wanda ya sha kaye da tazarar kusan ƙuri'u miliyan 4.4, ya ce tawagarsa za ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
Ya bayyana hakan ne bayan kotun koli ta kasar ta amince da tsawaita lokacin kada kuri'a da sa'o'i biyu a ranar zaben.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a babban birnin kasar, Brasília, bayan sanar da nasarar Lula, Bolsonaro ya ce ba zai yiwu a amince da sakamakon zaben ba saboda yadda abubuwan suka gudana.
Ya ce za su ɗauki matakin shari'a tare da neman a soke zaben.
A nasa bangaren, Lula ya bayyana cewa zai sauya salon tafiyar da gwamnati tare da bai wa jama'a damar taka rawa sosai wajen yanke shawarar da ta shafe su.
Ya kuma gode wa al'ummar Brazil saboda goyon bayan da suka ba shi, musamman matasa da ya ce sun fito kan tituna domin kare dimokuraɗiyya.
Lula ya samu gagarumar nasara
Nasarar Lula ta zo ne a wani lokaci da dama daga cikin ƙasashen Latin Amurka ke fuskantar sauyin siyasa.
Yaƙin neman zaben ya fi karkata kan matsalolin tsadar rayuwa, rashin tsaro da cin hanci da rashawa, wadanda suka kasance cikin manyan abubuwan da suka damu masu kada kuri'a.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa magoya bayan Lula sun yi murna a biranen Rio de Janeiro da Belo Horizonte bayan sanar da nasararsa, inda aka gan su suna rungumar juna, busa kahon motoci da rera wakokin murna.
Zaben na wannan shekara ya kuma kasance na musamman, domin shi ne karo na farko tun bayan dawo da zaben shugaban kasa kai tsaye a shekarar 1989 da dan takara ya lashe shugabancin kasar bayan ya zo na biyu a zagayen farko.
Katie ta yi murabus a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa Katie Zacharia za ta bar mukaminta na kakakin yada labarai na fadar White House, kwanaki biyar kacal bayan gudanar da taronta na farko da manema labarai cikin yanayi mai cike da suka.

Kara karanta wannan
Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 3 har lahira a Arewacin Najeriya
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wa manema labarai cewa ya gaya mata cewa ba lallai ne ta ci gaba da aikin ba idan ba ta so, yana mai cewa da shi ne a matsayinta, zai sake tunani kan matakin.
Zacharia ta fuskanci suka mai yawa bayan taronta na farko da manema labarai a ranar Talata, wanda bai kai mintuna 15 ba kuma ta amsa tambayoyi uku kacal.
Asali: Legit.ng

