Birane 5 Da Ke Karkashin Kasa, Wurin Da Suke Da Labaransu Masu Cike Da Al'ajabi

Birane 5 Da Ke Karkashin Kasa, Wurin Da Suke Da Labaransu Masu Cike Da Al'ajabi

Ba rade-radi bane, tabbas akwai wasu birane da ke karkashin kasa a duniya. Wasu daga cikin biranen nan sun kasance karni aru-aru kuma har a halin yanzu ana al'amuran rayuwa a cikinsu.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legit.ng ta tattaro muku labaran irin wadannan wuraren masu al'ajabi da kuma inda suke.

Birane 5 da ke karkashin kasa da labaransu masu cike da al'ajabi
Birane 5 dake karkashin kasa, wurin da suke da labaransu. Hoto daga REDA&CO, Richard Baker
Asali: Getty Images

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke mutum 8, sun kone coci da wasu gidaje a Kaduna

1. Derinkuyu, Cappadocia, Turkiyya

Birnin Capppadocia na nan a kasar Turkiyya kuma yana da birane kusan 36 da ke karkashin kasa, Momondo ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano birnin ne a 1963 kuma an bude shi jama'a na shiga a 1965. An gano cewa birnin Derinkuyu ne yafi kowanne zurfi a cikin biranen.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

An gano cewa ya samarwa jama'a 20,000 matsuguni a cikin shekarun da suka gabata. Yana da cibiyoyi daban-daban.

2. Shanghai Tunnels, Portland, Amurka

Yana nan a Portland, a Amurka akwai wani birni da ake kira da ramin Shanghai. Birnin da ke kasan kasa na Shanghai ana rade-radin wuri ne da ya kasance dabdalar masu garkuwa da mutane.

A halin yanzu wuri ne da ya zama na yawon bude ido. Yana da otal, mashaya da sauransu.

3. Naours, Faransa

Birnin Naours na nan a arewacin kasar Faransa kuma yana da kusan dakuna 300, History.com ta ruwaito.

Yana nan a karkashin kasa kusan nisan kafa 100 kuma an fara samar dashi ne a karni na uku a matsayin wurin hakar duwatsu na Romaniya domin mazauna kauyen na amfani dashi wurin buya yayin yaki.

Akwai gidajen biredi, wurin adana dawaki, rijiyoyi da sauran abubuwa da ake samu a birnin mai cike da abun mamaki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

4. Wieliczka Salt Mine, Poland

Wieliczka wurin hakar gishiri ne dake Poland kuma wani birni ne da ke karkashin kasa mai cike da abubuwan mamaki. Birnin dake da shekaru 1200 ya kasance yana samar da gishiri har zuwa 2007.

Ma'aikata a wancan lokacin suna amfani da gishirin da ake haka a wurin domin hada gumaka.

5. Birnin kasa na Beijing, China

Birnin yana nan a China kuma gwamnatin kasar China ce ta gina shi tun a 1960 saboda yaki, kamar yadda History.com ta ruwaito.

Yana kunshe da ramuka tare da dakuna. Akwai dakin kallo da ke da mazaunin mutum 1000 kuma an bude shi domin masu yawon bude ido da shakatawa tun wurin 2000.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke mutum 8, sun kone coci da wasu gidaje a Kaduna

A wani labari na daban, Gimba Kumo, tsohon sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai taba samun gayyata daga hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ba kafin ta ce tana nemansa a kan badakalar kudi har $65 miliyan yayin da yake manajan daraktan bankin gidaje na tarayya.

Kara karanta wannan

Manyan Abubuwa 5 Da Shugaba Tinubu Ya Aiwatar a Watansa Na Farko a Ofis

Kumo ya sanar da hakan a wata wasika da ya rubuta zuwa shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye mai kwanan wata 18 ga Mayun 2021.

A ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ICPC tace tana neman Kumo ruwa a jallo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a kan wata damfara da ake zarginsu da ita, jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel