MTN Ya Tabo Matsalar Yan Najeriya, Ya Fadi dalilin Karewar ‘Data’ da Wuri

MTN Ya Tabo Matsalar Yan Najeriya, Ya Fadi dalilin Karewar ‘Data’ da Wuri

  • MTN Nigeria ya ce abubuwan da masu amfani da data ke yi da manhajoji masu aiki a bayan fage na sa kuɗin intanet ƙarewa da sauri
  • Kamfanin ya musanta zargin satar kuɗin data, inda ya bayyana cewa saitunan waya da yadda mutane ke amfani da manhajoji ke ƙayyade yawan data da ake cinyewa
  • MTN ta shawarci masu amfani da intanet su kashe sauke fayiloli kai tsaye, rage ingancin bidiyo da bibiyar amfani da data domin rage kashe kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin MTN Nigeria ya danganta saurin ƙarewar data da masu amfani da intanet saboda yawan kallace-kallace.

MTN ya ce kallon bidiyo masu inganci, sauke abubuwa kai tsaye, manhajojin da ke aiki a bayan fage, ajiyar bayanai a gajimare da kuma ƙaruwar amfani da intanet.

Kara karanta wannan

An dauke matar da ta shigo da Ebola Najeriya, ta bar Abuja zuwa ƙasar waje

Dalilin da ya sa data ke karewa da wuri
Mata tana amfani da data a wayarta. Hoto: MTN.
Source: UGC

Hakan na cikin jawabi a wani taro mai taken “Data on Trial” da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, cewar Punch.

MTN ya musanta zargin satar data

Kamfanin ya musanta zargin cewa kamfanonin sadarwa na cire wa kwastomomi data da gangan.

MTN ya bayyana cewa mutane da yawa na amfani da data mai yawa ba tare da sani ba, saboda saitunan wayoyinsu da manhajojin da ke ci gaba da aiki ko da ba sa amfani da intanet a lokacin.

Babban manajan kula da ingancin sadarwa na MTN Nigeria, Mike Ndukwe, ya ce yawan data da ake amfani da ita ya danganta ne da ayyukan masu amfani da kuma saitunan na’urorinsu.

Ya ce:

“Ba ma satar data ɗinku. Duk da haka, mun fahimci yadda abin yake ji, musamman a yanzu da kowane kuɗi yake da muhimmanci. Amma gaskiyar magana ita ce, ba a cinye data ba tare da wani aiki ba, ko dai aikin da kuka yi ko kuma wayarku ce ta yi.”

Kara karanta wannan

Abin bakin ciki: Matashi ya kashe abokinsa da suke aiki wuri 1 kan gardamar siyasa

Ndukwe ya bayyana cewa manhajoji kamar TikTok, YouTube, Instagram da WhatsApp suna cinye data gwargwadon ingancin bidiyo, kunna bidiyo kai tsaye da kuma yawan sauke fayiloli.

A cewarsa, kallon bidiyon TikTok na tsawon daƙiƙa 15 na iya cinye tsakanin megabyte biyu zuwa 20, gwargwadon ingancinsa, yayin da kallon bidiyo mai ingancin HD ke buƙatar data fiye da kallon bidiyo mai ƙarancin inganci.

Ya ce saƙonnin WhatsApp na rubutu ba sa cinye data mai yawa, amma kallon hotunan status, bidiyo, saƙonnin rukuni da sauke fayilolin da manhajar ke yi kai tsaye na iya sa data ta ƙare fiye da yadda masu amfani suke tsammani.

Shawarar MTN ga yan Najeriya

Da yake amfani da misalin kunshin data mai girman gigabyte ɗaya, ya bayyana yadda sabunta manhajoji a bayan fage, ajiyar bayanai a gajimare da ayyukan tsarin waya za su iya cinye data ba tare da mai waya ya fara sauke wani abu da kansa ba.

Ya shawarci masu amfani da wayoyi su takaita sabunta manhajoji kai tsaye ta hanyar amfani da Wi-Fi, saita iyakar data, bibiyar na’urorin da ke haɗe da hotspot da kuma rage ingancin bidiyo.

Kara karanta wannan

Duk da ƙoƙarin Tinubu kan tsadar kaya, abinci na ci gaba da tashi a kasuwanni

Kojode ya kuma nuna wasu fasalolin wayoyi da ke ba masu amfani damar bibiyar data da kuma takaita rabawa da wasu na’urori, yana mai cewa fahimtar saitunan waya za ta taimaka wa ’yan Najeriya wajen sarrafa kuɗin data da suke saya.

MTN ya ba yan Najeriya hakuri

Mun ba ku labari a baya cewa kamfanin sadarwa na MTN ya gaggauta ba jama'a haƙuri biyo bayan karin kuɗin 'data' da akalla 200% a tsakiyar makon nan.

MTN ya lura da yadda jama'a su ka yi masa ca a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya sa ya fitar da sako domin kwantar da hankula.

A ranar Alhamis ne dai kamfanin ya fitar da sabon farashin 'data, kuma 15GB da ake saye a ₦2,000 ya tashi zuwa ₦6,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.