Sakon Gwamna Radda ga Mutanen Katsina kan Kisan Sheikh Masussuka
- Gwamna Dikko Radda ya bayyana alhininsa kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka, fitaccen malamin addinin Musulunci mai wa’azin zaman lafiya
- Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Katsina cewa za a gudanar da cikakken bincike domin hukunta wadanda suka aikata kisan
- Radda ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu, su ba jami’an tsaro hadin kai tare da kiyaye zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Gwamna Radda ya bayyana Sheikh Masussuka a matsayin mai kira ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin sakon ta'aziyyar da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026.
A cikin sakon ta’aziyyarsa, gwamnan ya fara da kalmar “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”, yana mai cewa ya yi matukar bakin ciki da mummunar rasuwar malamin.
Radda ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin
Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar Musulmi da dukkan wadanda wannan rashi mai radadi ya shafa.
Ya bayyana Sheikh Masussuka a matsayin malamin da ya samu girmamawa a cikin al’umma, musamman saboda kokarinsa na inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Radda ya ce gwamnati za ta tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano wadanda suka aikata kisan da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.
Radda ya bukaci a kwantar da hankula
Gwamna Radda ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu a wannan lokaci mai wahala na kisan malamin.
Ya bukaci jama’a su ba jami’an tsaro hadin kai domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali ko kawo cikas ga zaman lafiya.
Hakazalika, ya jaddada muhimmancin hadin kan al’umma da hukumomin tsaro wajen gano wadanda ke da hannu a kisan da kuma tabbatar da adalci.
Radda ya yi addu'a ga Sheikh Masussuka
A karshen sakon nasa, gwamnan ya roki Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa Sheikh Yahya Masussuka kurakuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyalansa, dalibansa da sauran masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.
Sakon ta'aziyyar na gwamnan na zuwa ne bayan wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun hallaka malamin a kofar gidansa da ke karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Source: Facebook
'Yan sanda sun fara farautar makasan Masussuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta fara farautar wadanda suka kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa Adamu Abubakar a karamar hukumar Dutsin-Ma.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an dabaru da na gudanar da ayyuka zuwa yankin domin kamo wadanda ake zargi.
Asali: Legit.ng

