Allah Ya Yi Wa Gogaggen Dan Jarida Dele Oni Rasuwa Yana Da Shekaru 73 a Duniya

Allah Ya Yi Wa Gogaggen Dan Jarida Dele Oni Rasuwa Yana Da Shekaru 73 a Duniya

  • Dele Oni, wani gogaggen dan jarida da ya samu karbuwa a gidan talabijin na Najeriya (NTA) ya rasu
  • Oni ya rasu ne a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni yana da shekaru 73 a duniya, kamar yadda dansa Dr. Ayodele Oni ya sanar
  • Marigayin ɗan jaridan Yarabancin ya shahara a tashar NTA 7 da Channel 10 a cikin shekarun 80s da 90s

Legas - Dele Oni, wani gogaggen dan jarida, mai yaɗa labarai a sashen Yarabanci na gidan talabijin na Najeriya (NTA), ya rasu.

Dele Oni ya yi fice sosai a tashar NTA Channel 7 da Channel 10 a cikin shekarun 80s da 90s.

Shehu Sani ya yi jimamin rasuwar shahararren dan jarida
Shehu Sani da wasu masu amfani da Tuwita sun yi jimamin mutuwar gogaggen dan jarida. Hoto: Nigerian Television Authority
Asali: UGC

Dansa ne ya sanar da labarin rasuwar a Tuwita

Legit.ng ta samu rahoto cewa Oni ya rasu ne a ranar Litinin 5 ga watan Yuni yana da shekaru 73 a duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Babban Rashi Na Kaninsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan sa, Ayodele Oni ne ya bayyana labarin rasuwar mahaifin nasa a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Ayodele ya rubuta:

"Idan ka kalli NTA Channel 7 & Channel 10, a cikin shekarun 80s zuwa 90s, tabbas za ka san Dele Oni (mahaifina), ɗan jarida da ke karanta labaran Yarabanci. Ya yi fice sosai a zamaninsa. Ya rasu a safiyar yau, yana da shekaru 73 a duniya."

Masu amfani da yanar gizo sun tattauna kan batun na rasuwar Dele Oni

Masu amfani da kafar sada zumunta ta Tuwita da suka samu labarin rasuwar ɗan jaridan sun nuna juyayinsu dangane da hakan.

Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ma na daga cikin waɗanda suka nuna alhininsu kan rasuwar, Shehu ya ce:

"Ya yi fice sosai, dama na kasance ina ta mamakin ko ina yake, Allah ya sa ya huta, ina muku ta'aziyya."

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba

@KemPatriot ne ya rubuta:

"Awwww Allah ya jikansa, yasa ya huta, Allah ya baka ikon jure rashinsa."

@woye1 kuma ya ce:

"Allah ya sa ya huta."

@Olusoga Owoeye ya rubuta:

"Ina taya ka baƙin ciki, na rasa mahaifina yana ɗan shekara 71 dan haka nasan irin yadda ake ji, fatan ya kasance tare da mala'iku, kuma Allah ya baku ikon jure rashin, Allah ba da haƙuri."

@EdimFriday1 ya ce:

"Tabbas ya bar abubuwan da za a daɗe ana tunawa da shi."

Ɗan uwan tsohon ministan shari'a ya rasu yana da shekaru 55

A wani labarin na daban, kun ji labarin rasuwar ƙanin Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a kuma atoni janar a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ɗan uwan Malamin, Dakta Khadi Zubairu Malami, mai kimanin shekaru 55, ya rasu ne da safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, a gidansa da ke birnin Kebbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel