Wani Bidiyon Dattijo Da Aka Yi Wa Kyautar Kudi Ya Fashe Da Kuka Ya Sosa Zuciya

Wani Bidiyon Dattijo Da Aka Yi Wa Kyautar Kudi Ya Fashe Da Kuka Ya Sosa Zuciya

  • Labarin wani tsohon soja kuma tsohom ɗan sanda wanda yayi ritaya a shekarar 2002 amma har yanzu ya kasa samun kuɗin fanshon sa ya sanya mutane da dama zubar da hawaye
  • Dattijon mai shekara 72 ya bayyana labarin sa ne ga wani wanda yayo hira da shi inda daga ƙarshe ya ɗauki (N3000) ya ba shi ya hau mota amma cikin mamaki sai ya fashe da kuka
  • Lokacin da dattijon ya karɓi kuɗin, sai hawayen farin ciki suka fashe daga idanun sa waɗanda suka sosa zuciyar mutanen dake kusa da shi

An daɗe da sanin irin halin da waɗanda suka sadaukar da rayuwar su wajen bautawa ƙasar nan suke shiga bayan sun aje aiki.

Labarin wani dattijo tsohon soja da ba a bashi kuɗin fanshon sa ba wanda @edithlipson ya sanya a TikTok ya yaɗu sosai.

Kara karanta wannan

Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Da Ba Zai Taba Mantawa Da Ita Ba a Rayuwarsa

Dattijo
Wani Bidiyon Dattijo Da Aka Yiwa Kyautar Kudi Ya Fashe Da Kuka Ya Sosa Zuciya Hoto: TikTok/edithlipson
Asali: UGC

A cikin bidiyon dattijon ya gayawa mai hira da shi cewa ya je bankin domin sanin halin da ake ciki dangane da sauran kuɗin fanshon sa da ba a biyaa shi ba tun shekarar 2002.

Dattijon mai shekara 72 a duniya yayi bayanin cewa yayi aiki lokacin yaƙin basasa amma daga baya koma aikin ɗan sanda har zuwa shekarar 2002, lokacin da yayi ritaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa an biya dukkanin kuɗin fansho na ɓangaren sojohi amma ba a biya shi kuɗin fanshon sa na aikin ɗan sanda ba inda nan ne ya fi ƙwashe shekaru yana aiki.

A yayin da ake cigaba da ji a jika kan ƙarancin kuɗi, dattijon yaje banki domim ya samu ƴan na sawa a aljihu inda aka ba shi lamba ta 141 domin jiran layi. A hakan ma har ya zuwa ƙarfe 11 bankin bai buɗe ba.

Kara karanta wannan

Likita Ya Faɗa Wa Wani Mutumi Kar Ya Kusanci Matarsa Saboda Abu 1, Da Suka Koma Gida Ya Ba Da Mamaki a Bidiyo

Budurwa Ta Sace Zuciyar Mahaifin Tsohon Saurayinta Bayan Raba Jiha Da shi

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koma soyayya da mahaifin tsohon saurayin ta bayan sun raba gari.

Budurwar dai ta yanke wannan ɗanyen hukuncin ne bayan ita da tsohon saurayin na ta suka rabu. Wannan abin ɗa tayi ya janyo cece-kuce sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel