Duk da Ana Surutu kan Mutum 1, Majalisar Kano Ta Gama Aiki kan Mutane 6 da Abba Ya Turo Mata
- Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin mutum shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar domin zama kwamishinoni
- Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, Farfesa Sani Lawan da Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa
- Sababbin kwamishinonin sun yi alƙawarin inganta tsaro, yaɗa ilimin kimiyya da fasaha da kuma yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin mutum shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf gabatar domin zama kwamishinoni a Majalisar Zartarwa ta jihar.
Majalisar ta tabbatar da naɗin ne yayin zaman da ta gudanar ranar Litinin ƙarƙashin jagorancin Kakakinta, Rt. Hon. Jibril Falgore.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa an amince da sababbin kwamishinonin ne bayan wani ƙuduri da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini, ya gabatar, wanda shugaban marasa rinjaye, Usman Abubakar, ya mara wa baya.
Sunayen sababbin kwamishinoni 6
Waɗanda majalisar ta tabbatar da naɗinsu sun haɗa da:
1. Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya
2. Hon. Ibrahim Namadi
3. Farfesa Sani Lawan
4. Hon. Muktar Ishaq Yakasai
5. Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa
6. Hon. Idris Garba Mustapha.
Dalilin tabbatar da nadin mutane 6
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar, shugaban masu rinjaye ya ce mutanen shida sun cika dukkan sharuddan da ake buƙata domin naɗa su kwamishinoni.
Ya bayyana cewa majalisar ta gamsu da ƙwarewarsu ta fuskar ilimi, gogewar aiki da kuma gudummawar da suka bayar wajen yi wa jama’a hidima.
Hussaini ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda aka tabbatar da naɗinsu sun taɓa riƙe muƙaman kwamishinoni a baya, yayin da wasu kuma suka riƙe manyan muƙaman gwamnati, ciki har da shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC).
Ya ce za a sanar da bangaren zartarwa sakamakon tantancewa da tabbatar da naɗin mutanen shida domin gwamnatin jihar ta raba musu ma’aikatun da za su jagoranta.
Yusha’u ya yi magana kan tsaro
Ɗaya daga cikin waɗanda aka tabbatar da naɗinsu, Air Commodore Salisu Yusha’u mai ritaya, ya yi alƙawarin haɗa kai da hukumomin tsaro da al’ummomin yankunan jihar Kano domin ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Source: Facebook
Yusha’u, wanda ya bayyana kansa a matsayin masani kan harkokin tsaro, ya ce haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai wajen tinkarar ƙalubalen tsaro da suka shafi al’ummomi daban-daban a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Abba ya dawo da tsohon kwamishina
Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Ibrahim Ali Namadi tare da wasu mutane biyar ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin naɗa su kwamishinoni.
Ibrahim Ali Namadi, tsohon kwamishinan sufuri ya yi murabus bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan bayar da belin wani mutum da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Asali: Legit.ng

