Iran Ta Kai Zazzafan Farmaki kan Tashar Jirgin Kasa, Cibiyar Fasaha da Sansanin Soji a Isra'ila

Iran Ta Kai Zazzafan Farmaki kan Tashar Jirgin Kasa, Cibiyar Fasaha da Sansanin Soji a Isra'ila

  • Ƙasar Iran ta kai farmaki da makamai masu linzami kan muhimman wurare a birnin Beersheba da ke Kudancin Isra'ila
  • Rahotanni sun bayyana cewa harin ya lalata wani ɓangare na tashar jirgin kasa da ke tsakiyar birnin, wanda ya jawo aka dakatar da aiki
  • Wannan dai na zuwa ne bayan sojojin juyin juya halin Iran sun sanar kai hare-hare zagaye na biyu kan biranen Isra'ila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Rahotanni daga Isra’ila sun tabbatar da cewa makami mai linzami da aka harbo daga Iran ya faɗa kusa da Beersheba, birni da ke kudancin ƙasar.

Farmakin makamin ya taɓa cibiyoyi masu muhimmanci irin su ofishin Microsoft, cibiyar bincike da fasaha ta Gav-Yam Negev da kuma sansanonin sojin Isra’ila.

Iran na ci gaba da kai hare-hare.
Iran ta lalata muhimman wurare da ta harɓe makami kasar Isra'ila Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Aljazeera ya tabbatar da cewa Iran ta lalata wani ɓangare na tashar jirgin ƙasa ta tsakiyar birnin Beersheba na ƙasar Isra'ila wanda ya jawo rufe wurin gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iran ta lalata tashar jirgin ƙasa a Isra'ila

Wannan tashar jirgin ƙasa na da muhimmanci sosai ga zirga-zirgar jama'a a birnin na Isra'ila, lamarin da ke ƙara nuna illar da ake yi wa ƙasar.

Haka zalika hotuna daga yankin sun nuna cewa Iran ta fara lalata ofishin Microsoft da ke cikin cibiyar fasaha ta 'Gav-Yam Negev Advanced Technologies Park'.

Wannan cibiyar fasaha ta zamani, wanda ke kusa da Jami’ar Ben-Gurion, na da matuƙar muhimmanci wajen bincike a fannonin kimiyyar bayanai, fasahar kera na'ura mai aiki da kanta da wasu manyan fasahohi.

Mutane 7 sun samu rauni a harin Iran

A cewar rahotan BBC News, akwai mutane bakwai da suka ji raunuka sakamakon harin, kuma an gaggauta ba su taimakon farko.

An ruwaito cewa Iran ɗin ta kai harin ne da sassafe tun kafim buɗe ofisoshi, wanda ya sa ba a samu mutane da yawa a wuraren ba a lokacin da makamin ya faɗo.

Yankin kudancin Isra’ila da abin ya shafa ba shi da yawan jama’a kamar sauran yankuna, lamarin da ya taimaka wajen rage asarar rayuka.

Jagoran addinin na kasar Iran.
An rufe tashar jirgin kasa a Isra'ila bayan Iran ta sake kai hare-hare Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Wannan hari dai ya ƙara nuna yadda rikicin Isra'ila da Iran ke ƙara ƙamari yayin da ake dakon matakin shugaban Amurka, Donald Trump zai ɗauka.

Iran dai ta zafafafa kai hare-hare kan cibiyoyin da ke da tasiri a fannin fasaha, bincike, da harkokin sojoji a ƙasar Isra'ila.

Iran ta kai farmaki a asibitin Soroka

A wani rahoton, kun ji cewa wani harin makami mai linzami daga Iran ya yi mummunan barna a wurare hudu a tsakiyar Isra’ila, ciki har da asibitin Soroka.

Bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna hayaki ya turnake asibitin Soroko yayin da mutane ke kururuwa suna neman dauki.

Rahotannin sun tabbatar da cewa an kai hari sau uku a wasu sassa na kasar Isra'ila a daidai lokacin da aka farmaki babban asibitin, lamarin da ya jefa mutane cikin fargaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262