Tarihi bai Manta ba: China Ta Tunawa Duniya yadda Iran Ta Buga Gwagwarmaya a Baya

Tarihi bai Manta ba: China Ta Tunawa Duniya yadda Iran Ta Buga Gwagwarmaya a Baya

  • Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gabatar da shawarwari hudu da suka shafi rikicin Gabas ta Tsakiya, yana mai kira da a dakatar da fadan haka
  • Xi ya ce hanyoyin diflomasiyya da tattaunawa sune mafita, tare da bukatar hadin kan kasashen duniya wajen samar da zaman lafiya
  • Ya tunatar da duniya cewa lura da gwagwarmayar baya da Farisawa mutanen Iran suka yi alama ce ta nuna jajircewa da kuma taurin zuciya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - A yayin da rikicin Isra’ila da Iran ke kara kamari, tare da alamun shiga tsakani daga Amurka, kasar China ta yi magana.

China ta bayyana matsayinta tare da gabatar da muhimman shawarwari guda hudu domin dakile rikicin da ke barazana ga zaman lafiyar duniya.

Xi Jinping ya ce Iran ta saba gwagwarmaya a duniya
Shugaba Xi Jinping ya ce Iran ta saba gwagwarmaya a duniya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaba Xi Jinping ya yi magana ne a ranar 19 ga Yuni, a shafinsa na X, inda ya jaddada cewa yin sulhu da kawo karshen fada ya zama wajibi, tare da kare rayuwar fararen hula.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya ce dole ne a bude hanyar tattaunawa da sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici, yayin da ya kamata kasashen duniya su rungumi kokarin samar da mafita mai dorewa.

China: Hanyoyin sasanta Iran da Isra'ila

1. A cewar Xi Jinping, abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne a dakatar da rikici domin kare rayukan mutane.

“Kawo karshen rikicin cikin gaggawa ya zama wajibi,”

Inji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China a X.

2. Shugaban ya kuma jaddada cewa kare rayukan fararen hula ta fi komai muhimmanci a halin yanzu.

3. Xi ya ce hanyar tattaunawa ce kadai mafita a wannan rikici, yana mai kiran bangarorin biyu da su bude kofar fahimtar juna da sasanci.

4. Haka kuma, ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa da su kara himma wajen tallafa wa kokarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran da Isra'ila: China ta soki kasar Amurka

Yayin da Amurka ke nuna sha’awa shiga yakin da ke ci tsakanin Isra’ila da Iran, kasar China ta sha alwashin kasancewa mai shawo kan matsalar bangarorin.

Wasu rahotanni na nuna cewa Amurka na iya shiga rikicin kai tsaye, lamarin da Xi Jinping ke kallon barazana ce ga kwanciyar hankali a duniya.

Xi ya ce China na kokarin bayyana kanta a matsayin kasa mai neman ci gaba da zaman lafiya, tana kokarin kasancewa kasa ta farko da za ta samu ci gaba mai dorewa a duniya.

China ta ce Iran na da tarihin gwagwarmaya

Xi Jinping ya tunatar da duniya cewa Iran – wato kasar Farisa ta da – ta sha tsallake mawuyacin hali a tarihi, ciki har da lokacin mamayar Alexander.

Bincike ya nuna cewa Alexander ya yi mamaya a tsakanin shekara ta 334 zuwa 330 kafin haihuwar Annabi Isa (AS).

Sanata ya hango yakin duniya na 3

A wani rahoton, kun ji cewa kun ji cewa Sanata Ben Murray-Bruce ya ce ya hango yakin duniya na 3 na tafe.

Sanatan ya yi bayani ne yayin da aka shafe kwanaki ana fafatawa tsakanin Iran da Isra'ila ba tare da samo mafita ba.

Ya kara da cewa Najeriya za ta kasance cikin zaman lafiya ko da yakin ya barke kuma mutanen Amurka, Iran da Isra'ila za su yi gudun hijira zuwa Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng