Ebola: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan 'Yiwuwar' Hana Taruwar Jama'a
- Ministan lafiya, Ali Pate, ya ce gwamnatin tarayya ba ta haramta tarukan siyasa masu yawan jama’a ba duk da bullar cutar Ebola a Najeriya
- Ali Pate ya ce gwamnati za ta tuntubi masana lafiya tare da amfani da hujjojin kimiyya kafin yanke shawarar hana tarukan jama’a
- An tabbatar da bullar Ebola a Abuja, inda wata mata da ta dawo daga Uganda ta kamu, yayin da ake bibiyar mutum 44 da suka yi mu’amala da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan lafiya da walwalar jama’a na Najeriya, Ali Pate, ya yi magana game da sake dawowar cutar Ebola a Najeriya.
Pate ya ce gwamnatin tarayya ba ta haramta manyan tarukan siyasa ba bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a ƙasar.

Source: Facebook
Ebola: Abin da ma'aikatar lafiya ke shiryarwa
Pate ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai kan halin da ake ciki game da cutar Ebola a Abuja, cewar TheCable.
Ya ce ma’aikatar za ta tuntubi masana da hukumomin da abin ya shafa, sannan ta dogara da hujjojin kimiyya da la’akari da lafiyar jama’a kafin yanke shawarar takaita manyan taruka.
Ya ce:
“A halin yanzu, babu wata alama da ke nuna cewa akwai bukatar mu sauya tsarin manyan tarukan da aka riga aka shirya gudanarwa.”
Sai dai ya ƙara da cewa idan yanayin cutar ya sauya, gwamnati za ta sake duba matakin da ya dace ta hanyar tuntubar masana da suka dace.
Ministan ya shawarci ’yan Najeriya da su riƙa dogaro da bayanan ƙwararrun masana lafiya masu sahihanci, tare da guje wa yaɗa jita-jita da bayanan ƙarya game da barkewar cutar.
Ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da su guji mayar da batun lafiyar jama’a siyasa, yana mai cewa lafiya batu ne da ya haɗa ’yan Najeriya ba tare da la’akari da siyasa, ƙabila ko addini ba.
Pate ya ce:
“Duk wani mataki da za a ɗauka zai dogara ne kawai kan kimiyya, hujjojin lafiyar jama’a da kuma abin da ake ganin ya fi dacewa da al’ummar Najeriya.”

Source: Twitter
Yadda Ebola ta sake ɓulla a Najeriya
A ranar Talata, Ali Pate ya tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya (FCT), inda ya bayyana cewa ana bin diddigin mutum 44 da suka yi kusanci da majinyaciyar domin hana yaɗuwar cutar.
Ministan ya ce majinyaciyar mace ce da ta dawo Najeriya kwanan nan ta jirgin sama daga ƙasar Uganda.
Ya bayyana cewa an kwantar da ita a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja, inda ta shafe kwanaki tana samun kulawa kafin a tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar Ebola.
Ebola: Gwamnati ta kwantarwa yan Najeriya hankali
Mun ba ku rahoton cewa Ministan Lafiya ya bukaci ’yan Najeriya kada su firgita kan bullar cutar Ebola, yana mai cewa gwamnati na da ƙarfin dakile ta.
Wata mata da ta shigo Najeriya daga Uganda ta kamu da cutar, lamarin da ya sa aka fara bin diddigin mutanen da ta yi hulɗa da su.
Gwamnati na aiki tare da Uganda da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) domin hana cutar yaɗuwa.
Asali: Legit.ng

