Gwamna Abba Ya Bayyana Irin Kuri'un da Mutanen Kano Za Su ba Tinubu a Zaben 2027

Gwamna Abba Ya Bayyana Irin Kuri'un da Mutanen Kano Za Su ba Tinubu a Zaben 2027

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Kano ya tabbatar jihar ta samar da mafi yawan ƙuri’u ga Shugaba Bola Tinubu
  • Gwamnan ya bukaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan nasarorin shugabannin APC maimakon zage-zage da musayar yawu
  • Ya yi kira da a ƙara ƙaimi wajen wayar da kan masu zaɓe da kuma jawo goyon bayan jama’a a matakin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bukaci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC da su yi aiki tukuru.

Gwamna Abba ya bukaci su tashi tsaye domin tabbatar da cewa Kano ta samar da mafi yawan ƙuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

An shirya hallaka Atiku ana tunkarar zaben 2027? APC ta magantu

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a fdr gwamnatinsa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a Jihar Kano.

Gwamna Abba ya fadi tsarin kamfe

Ya buƙaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan nasarorin da shugabannin jam’iyyar suka samu, maimakon shiga zagi da musayar yawu da yan adawa.

“Za mu gudanar da yaƙin neman zaɓe ne bisa abubuwan da shugabannin APC suka yi, ba yaƙin neman zaɓe mai cike da zagi ba,” in ji gwamnan.

Ya ƙalubalanci mambobin kwamitin da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a matakin ƙasa, tare da isar da saƙon jam’iyyar ga masu zaɓe.

Kano za ta ba Tinubu kuri'u

Abba Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa Kano za ta iya samun mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa wa Tinubu a faɗin ƙasar.

“Kano ya kamata ta samar da ƙuri’u masu yawa ga Shugaba Tinubu. Yawan ƙuri’un da APC za ta samu a Kano ya kamata ya zama mafi yawa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Mawakin siyasa ya watsa wa Abba Kabir kasa a ido kan saka shi a kwamitin kamfe

"Hakan zai yiwu idan kun fita kun gudanar da yaƙin neman zaɓe yadda ya kamata,” in ji shi.
Abba da Tinubu.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Abba ya jinjinawa yan kwamitin kamfe

Gwamnan ya bayyana mambobin kwamitin a matsayin sojojin APC, inda ya buƙace su da su nuna jajircewa, ladabi da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukansu.

“Mambobin wannan kwamitin sojojin APC ne, kuma ina kira gare ku da ku sauke nauyin da ke kanku cikin jajircewa, tare da yin aiki domin samun nasarar jam’iyyar,” in ji Abba.

Ya kuma buƙaci kwamitin ya yi aiki tare domin ƙarfafa goyon bayan jama’a ga APC a Kano, tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓuka masu zuwa.

Abba ya ce Arewa na tare da Tinubu

Kun ji cewa Gwamna Abba ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa Arewa za ta mara masa baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana Kano a matsayin jihar Arewa da ke samar da mafi yawan ƙuri’u, yana mai cewa za ta jagoranci sauran jihohin yankin wajen ƙara yawan masu fitowa zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262