'Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Dan Takarar Jam'iyyar Su Kwankwaso, An Kashe Mutum 1
- ’Yan sanda a Ebonyi sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu uku bayan wani hari da ake zargin an kai wa ayarin motocin ɗan takarar NDC
- Ɗan takarar NDC a mazabar Ezza South ya ce wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai musu hari tare da ƙona motarsa kirar Toyota Hilux
- Offia-Nwali ya yi kira ga matasa da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu na kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi, Nigeria - Rundunar ’yan sanda a Jihar Ebonyi ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya yayin da wasu da ake zargin yan daba ne suka farmaki ayarin dan takarar NDC na Majalisar dokokin Ebonyi.
Rundunar yan sandan ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu mutum 3 a harin da aka kai wa dan takarar.

Source: Twitter
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Joshua Ukandu, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a Abakaliki, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Yan aanda sun mai dauki
Ukandu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma ranar Alhamis da ta gabata a garin Amaezekwe da ke Ƙaramar Hukumar Ezza South ta jihar Ebonyi
Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa kan wani rikici da ya ɓarke a garin, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin domin kai dauki da shawo kan lamarin.
“Da jami’an yan sanda suka isa wurin, sun tarar da mutane huɗu da raunukan harbin bindiga da kuma wata mota da aka ƙona.
“An tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa a asibiti, yayin da sauran ukun ke samun kulawar likitoci,” in ji shi.
Dan takarar NDC ya yi martani
A nasa ɓangaren, ɗan takarar NDC a mazabar Ezza South a majalisar dokokin jihar, Mista Offia-Nwali, ya ce wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai wa ayarin motocinsa hari tare da ƙona motarsa kirar Toyota Hilux.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abakaliki, Offia-Nwali ya ce shi da sauran mutanen da ke tare da shi sun tsira ba tare da sun samu rauni ba.

Source: Original
Ya nuna alhininsa ga waɗanda harin ya shafa, sannan ya buƙaci matasa a jihar Ebonyi da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu na kansu.
“Babu wani burin siyasa da ya kai darajar rayuwar matashi,” in ji shi.
NDC ta zargi APC da kwace mambobinta
Kun ji cewa jam’iyyar NDC ta zargi APC da amfani da kuɗi, muƙaman siyasa da sauran abubuwan more rayuwa wajen jawo wasu ’yan takararta su sauya sheƙa.
Jam’iyyar adawan ta ce tana sane da abin da ta kira yunƙurin APC mai mulki na shawo kan wasu ’yan takararta su fice daga cikinta.
Zargin ya biyo bayan murabus ɗin Ibrahim Kashim, ɗan takarar gwamnan Bauchi na NDC, da kuma sauya sheƙar Sanata Rufai Hanga zuwa APC
Asali: Legit.ng
