Yaron Obasanjo Ya Fanɗarewa Ubansa, Ya Kama Layin Tazarcen Tinubu a 2027

Yaron Obasanjo Ya Fanɗarewa Ubansa, Ya Kama Layin Tazarcen Tinubu a 2027

  • Ɗan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Olujonwo, ya shiga ƙungiyar Tinubu Must Stay domin tallafa wa ci gaba da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Olujonwo ya ce ana yaɗa bayanan ƙarya kan nasarorin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ɗalibai suna samun rance, yayin da ake gina ababen more rayuwa
  • Shugabannin ƙungiyar sun yi gargaɗin cewa sauya manufofin tattalin arziki na iya rage amincewar masu zuba jari tare da kawo cikas ga ci gaban Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

ABUJA: Olujonwo Obasanjo, ɗan tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya shiga ƙungiyar magoya bayan Bola Tinubu.

Olujonwo ya shiga ƙungiyar ce da aka fi sani da Tinubu Must Stay, domin inganta fahimtar jama'a kan manufofin Shugaba Bola Tinubu.

Tinubu ya sake samun goyon baya daga dan Obasanjo
Shugaba Bola Tinubu a taron majalisar zartarwa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Gudunmawar da Olujonwo ya ba Buhari

Kara karanta wannan

Tinubu ya jingine bambancin siyasa, ya aika da muhimmin sako ga Kwankwaso

Olujonwo, wanda yake shugaban ƙungiyar Buhari Youth Organisation (BYO), shugaban Project One Nigeria, kuma babban mataimaki na musamman ga gwamnan Ogun kan harkokin gidaje, ya samu tarbar shugabannin TMS a wani taro da aka gudanar a Abuja, cewar Vanguard.

Da yake bayyana dalilin shiga ƙungiyar, Olujonwo ya ce kasancewarsa tare da jam'iyya mai mulki tun da daɗewa da fahimtarsa kan tarihin gyare-gyaren Najeriya ne suka sa ya yanke wannan shawara.

Ya ce:

“Na kasance cikin APC tun shekarar 2014. Ina nan lokacin da mahaifina ya karɓi marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin kafa wannan tafiya. Ni ba sabon shiga jam'iyyar ba ne.”

Ya bayyana cewa ana karkatar da bayanai game da muhimman nasarorin gwamnatin yanzu, lamarin da ya sa ake buƙatar ƙarin bayani domin jama'a su fahimci manufofin gwamnati yadda ya kamata.

Ya ce:

“Akwai hayaniya sosai a wajen, kuma mutane suna karkatar da abin da ke faruwa. ASUU ba ta shiga yajin aiki ba. Ɗalibai suna samun rance. Najeriya ta zama babbar filin gine-gine, kuma ta sake zama wurin da masu zuba jari ke sha'awa. Waɗannan abubuwa ne da ya kamata mu tallata.”

Kara karanta wannan

Tinubu na da abin da zai fada wa yan Najeriya su zaɓe shi a 2027? Baba Ahmed ya yi magana

Tinubu ya sake samun karfi a siyasa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Kashifu Inuwa ya yaba wa dan Obasanjo

Da yake maraba da shi cikin ƙungiyar, mai kula da harkokin TMS na ƙasa, kuma darakta-janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, ya ce tarihin iyalinsa zai taimaka masa wajen fahimtar muhimmancin gyare-gyaren tattalin arziki.

Inuwa ya kwatanta manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu da sauye-sauyen sassauta harkokin tattalin arziki da gyaran bankuna da aka fara a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Obasanjo.

Ya ce:

“Ka taso ne a cikin iyalin da suka jagoranci zangon gyare-gyare na biyu a Najeriya. Sassauta harkokin sadarwa da gyaran bankuna sun kafa tubali mai ƙarfi. Saboda ka taso a wannan iyali, ka fahimci abin da gyare-gyare ke nufi.”

Inuwa ya yi gargaɗin cewa sauya manufofin gwamnati na kawo cikas ga ci gaba na dogon lokaci tare da raunana amincewar masu zuba jari daga ƙasashen waje, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Tinubu ya yi yabo ga ADC, ya fadi alherin da ta yi masa

Ana zargin an cire liman saboda Tinubu

A baya, an ji cewa ana fargabar an cire Imam Dahiru Abubakar daga limanci bayan zargin yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin wa’azi bayan salloli.

Kwamitin masallacin ya bayyana cewa ya sha gargaɗin limamin kan mayar da masallaci dandalin siyasa.

Ana zargin limamin ya kuma nemi a sauya sunan masallacin zuwa “Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu”, amma kwamitin ya ƙi amincewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.